Guardiola ya sha kashi a hannun Slot gida da waje a bana

Pep Guariola

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester City ta yi rashin nasara da ci 2-0 a hannun Liverpool a wasan Premier League da suka buga ranar Lahadi a Etihad.

Mohamed Salah ne ya fara cin ƙwallo a minti na 14 da fara wasan, kuma na 16 da ya zura a raga a karawar waje na 26 jimilla a bana kenan.

Ɗan wasan tawagar Masar ya yi kan-kan-kan da bajintar Kevin Phillips a 1999-00 da kuma Harry Kane a 2022-23 da suka zura ƙwallo 16 kowanne a waje.

Liverpool ta kara na biyu a raga ta hannun Dominik Szoboszlai tun kan hutu, kuma Salah ne ya bashi ƙwallon

Haka kuma Salah ya kafa tarihin zama na farko da yake da hannu a cin ƙwallo 40 ko fiye da haka a kaka biyu a Premier League.

Ya fara da cin ƙwallo 32 ya bayar da 10 aka zura a raga a 2017/18, sai a 2024/25 da ya ci 25 ya kuma bayar da 16 aka zura a raga.

Liverpool ta yi wa City gida da waje a bana, bayan da ta fara cin 2-0 a Anfield ranar 1 ga watan Disambar 2024.

Da wannan sakamakon Arne Slot ya ci wasa 24 daga karawa 27 a lik da kofuna, wanda ya doke Guardiola a Anfield da Etihad a bana a Premier League.

Haka kuma Liverpool ta yi karawa ta 23 ba tare da an doke ba, wadda ta yi bajintar wasa 44 ba tare da rashin nasara ba tsakanin Janairun 2019 zuwa Fabrairun 2020.

Liverpool ta ci gaba da zama ta ɗayan teburi da maki 64, bayan buga wasa 27, ta bai wa Arsenal tazarar maki 11 tsakani.

Ranar Asabar Arsenal ta yi rashin nasara 1-0 a hannun West Ham a Emirates, tana da maki 53, bayan karawar mako na 26.

City ta ci gaba da zama ta huɗun teburi da maki 44, bayan wasan mako na 26 da tazarar maki 20 tsakaninta da Liverpool.

Irin haka ta faru a watan Yulin 2020 da Liverpool ta bai wa City mai rike da Premier tazarar maki 20, sannan ta lashe babban kofin tamaula na Ingila.