Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man City na son Amorim ya gaji Guardiola, Isak ya sanya ƙungiyoyin jiran ko-ta-kwana
Ruben Amorim na cikin jerin sunayen wadanda za su iya karbar Manchester City idan Pep Guardiola ya bar kungiyar, Manchester United na zawarcin Alphonso Davies, Barcelona na zawarcin Romeo Lavia da Carney Chukwuemeka.
Manchester City na tunanin ɗauakr kocin Sporting Ruben Amorim, mai shekara 39, a matsayin kocinta na gaba idan Pep Guardiola, mai shekara 53, ya bar kungiyar idan kwantiraginsa ya kare a karshen kakar wasa ta bana. (Guardian)
Dan wasan baya na Bayern Munich na Canada Alphonso Davies, mai shekara 23, shi ne babban dan wasan da Manchester United za ta yi zawarci a bazara mai zuwa. (Sky Germany)
Barcelona na iya zawarcin dan wasan tsakiyar Belgium Romeo Lavia da dan wasan Ingila Carney Chukwuemeka, mai shekara 20, daga Chelsea a watan Janairu. (Sports Espanya)
Dan wasan gaban Sweden Alexander Isak, mai shekara 25, ya sanya kungiyoyi ciki har da Arsenal cikin shirin ko-ta-kwana yayin da yake ci gaba da dagewa kan rattaba hannu kan sabon kwantaragi a Newcastle. (talkSPORT)
An gwada lafiyar dan wasan tsakiya na Senegal Cheikhou Kouyate, mai shekara 34 a Leeds ranar Talata bayan ya tashi daga Nottingham Forest. (Football Insider)
Paris Saint-Germain ta ci gaba da neman dan wasan gaban Ingila Marcus Rashford, mai shekara 26 daga Manchester United bayan watsi da bukatarsu a bazara. (Team talk)
Chelsea ba ta shirya sayar da dan wasan gabanta dan Faransa Christopher Nkunku, mai shekara 26 ba, yayin da ake alakanta shi da Paris St-Germain. (Football Insider)
Tottenham da Crystal Palace duk suna zawarcin dan wasan Lille mai shekara 21 da kuma dan wasan Iceland Hakon Arnar Haraldsson. (Football Transfers)
An rage farashin golan Espanyol dan kasar Sipaniya Joan Garcia, mai shekara 23, wanda Arsenal ta nema a bazara, zuwa Yuro miliyan 25 (£20.83m). (Mundo Deportivo)
Akwai yuwuwar Manchester City ta bukaci a biya dan wasan gaba na Norway Erling Haaland, mai shekara 24, kudin siyan dan wasan gaba na Real Madrid ko Barcelona. (TeamTalk)
A halin yanzu, City ta bi sahun Chelsea, Arsenal da Tottenham wajen zawarcin dan wasan Shakhtar Donetsk da Ukraine Georgiy Sudakov, mai shekara 22. (I Sport)