Ko za a iya cewa gasa ta ƙare, yaushe Liverpool za ta ɗauki kofin Premier?

Asalin hoton, OTHERS
Bisa ga dukkan alamu ba makawa Liverpool ta kama hanyar ɗaga kofin Premier na bana in dai ba wani gagarumin sammatsi ba - bayan da ta ƙara kankane matsayinta na ɗaya a tebur da tazarar maki 13.
Babu wata ƙungiya a tarihin babbar gasar ta Ingila, tun daga kakar 1888-89, da ta taɓa yin wannan fintinkau a wannan mataki na gasar kuma a ce ba ta ɗauki kofin ba.
"Abin ya fara tashi daga gasa ya zama tamkar tattaki ko ba haka ba ne?" in ji gwani Gary Lineker, mai yi wa BBC sharhin ƙwallon ƙafa.
Duk tsawon wannan kakar Liverpool ta yi rashin nasara ne sau ɗaya kawai a gasar ta Premier - sannan a ranar Laraba ta caskara Newcastle 2-0.
Mai bi mata a baya- a baya, Arsenal ta zubar da maki a dukkanin wasanninta biyu na baya-bayan nan ciki har da wanda ta yi canjaras ba ci da Nottingham Forest.
Kociyan Liverpool Arne Slot ya ce: "Har yanzu da sauran tafiya, wasa 10 ba nan ba ne...
"Yanzu 'yanwasan suna da hutu, daga nan za mu mayar da hankali kan wasanmu na Zakarun Turai da Paris St-Germain fiye da yadda muka mayar da hankali a kan teburin Premier." In ji kociyan.
Ko kociyan Arsenal Mikel Arteta, yanzu dole ya san cewa kusan kasuwa ta riga ta ci ta cinye - ta tashi - to amma kafin wasansu da Forest ya ce shi bai sallama ba - bakin rai bakin fama.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bayan wasan na Forest, kociyan na Gunners ya gaya wa BBC cewa - haka abin yake ba bambanci mako ɗaya baya, da mako biyu baya, da ma wata uku baya. Ya ce abin kawai da za su yi yanzu shi ne su tabbatar suna cin wasanninsu su ga maki nawa za su samu - kenan dai har yanzu, Artetan bai sallama ba - yana ganin cinta.
To amma tsohon ɗanwasan gaba da gefe na Liverpool Steve McManaman, ya ce ai babu wata tantama ba wata tababa Liverpool a wannan ƙadami tamkar wani ingarman doki ne da ya kama hanyar cin gasa ba mai shiga gabansa sai dai a hangi ƙurarsa".
Ya ƙara da cewa: "Duk sauran ƙungiyoyin sai zubewa suke suna taimaka wa Liverpool ɗin."
Forest na ta uku a tebur da bambancin maki shida a bayan Arsenal, ita ma kuma Manchester City - wadda sau huɗu tana cin kofin na Premier a jere - na bayan Forest ɗin da maki ɗaya.
A tarihi ƙungiya ɗaya ce kawai ta taɓa wannan fintinkau da maki 13, kuma ba ta ɗauki kofin na Premier ba - lokacin da ƙiri-da-musu Manchester United na ji tana gani kuma Arsenal ta yi gaba da kofin a kakar 1997-98 - to amma wannan tun a farkon kakar ne Utd ɗin ta bayar da tazarar da ta zama tamkar sammakon-bubukuwa.
BBC ta yi nazari a kan lokacin da Liverpool ɗin za ta iya cin kofin na Premier nata na biyu ta kuma kafa tarihin da ya yi daidai da na 20 a gaba ɗaya.
Wane lokaci ne Liverpool za ta iya zare kofin?
Ba zai zama riga-mallam-masallaci ba a ce ƙungiyar ta Anfield, ta zama zakarun Premier masu jiran-gado a yanzu - magana ce kawai ta yaushe amma ba idan har ba.
Kamfanin ƙididdiga kan harkokin wasanni na Birtaniya- Opta- ya ce akwai yuwuwa kashi 98.7 cikin ɗari Liverpool ce za ta ɗauki kofin na Premier, yayin da Arsenal ke da dama ta kashi 1.3 cikin ɗari.
Liverpool ta yi wa Arsenal fintinkau da tazarar maki 13, yayin da ya rage wasa 10 a kammala gasa - kodayake Arsenal na da ragowar 11.
Idan har Liverpool ta ci gaba da wannan tazara ta maki 13, wannan zai sa ta ci kofin da ragowar wasa huɗu a nade tabarmar gasar - ranar 26 ga watan Afirilu kenan a wasanta da Tottenham.
To amma idan Arsenal ta ci kwantan wasanta ɗaya ta kuma yi daidai da sauran sakamakonta to Liverpool, za ta ɗauki kofin a ƙarshen mako mai zuwa a wasanta da Chelsea.
Idan har haka ta tabbata wasansu na farko a matsayin zakarun Premier zai kasance a gida da Arsenal, wadda za ta iya musu rakiyar shiga fili a matsayin zakaru.
Saboda cigaban da suke samu a gasar Zakarun Turai da kuma matsayinsu a gasar kofin Carabao na wasan ƙarshe da Newcastle da kuma hutun da za a iya na wasannin ƙasashe, Liverpool za ta yi wasa ɗaye ne kawai na Premier a watan Maris.
Lokaci mafi kusa da Liverpool za ta iya ɗaukar kofin na Premier a ƙididdiga shi ne makon farko na Afirilu.
Idan Liverpool ɗin ta ci wasanninta uku na gaba kuma aka doke Arsenal a wasanninta huɗu na gaba kuma ƙungiyoyin da ke bayansu suma suka zubar da maki 'yan ƙalilan, to Reds za su zare kofin ranar 5 ga watan Afirilu.












