Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man City ta kammala daukar Gvardiol daga RB Leipzig
Manchester City ta kammala sayan dan wasan bayan Croatia Josko Gvardiol kan kwantiragin shekara biyar daga RB Leipzig kan Yuro miliyan 90 (£77m).
Shi ne dan wasan baya na biyu mafi tsada a duniya, bayan Harry Maguire, wanda ya koma Manchester United kan fam miliyan 80 daga Leicester City a shekarar 2019.
Tauraruwar Gvardiol - mai shekara 21 - ta haska a kakar wasa biyu da ya yi a Leipzig bayan ya koma daga Dynamo Zagreb a watan Yulin 2021.
Gvardiol - wanda ya buga wa Croatia wasa sau 21 kuma ya taimaka wa kungiyarsa ta ta uku a gasar cin kofin duniya ta 2022 , kuma ta zo ta biyu a gasar Nations League ta bana - zai sanya riga mai lamba 24.
Ya taimaka wa RB Leipzig ta lashe kofin Jamus a kakar wasanni biyu da ya yi tare da su da kuma samun gurbin shiga gasar zakarun Turai sau biyu.
Gvardiol yana cikin kungiyar Leipzig da ta kai wasan kusa da na karshe a gasar Europa a shekarar 2021-22, inda a karshe suka sha kashi a hannun Rangers da ci 3-2.
Kungiyarsa ta Leipzig ta kare a matsayi na uku a rukuninsu a gasar cin kofin Zakarun Turai da City ta jagoranta a shekarar 2021-22 kuma ta sha kashi da ci 8-1 a wasanni biyu a hannun City a gasar zagayen 'yan 16 a kakar wasan da ta wuce, ciki har da rashin nasara da ci 7-0 a filin wasa na Etihad.