Rashford ya yi hatsari a mota a daren ranar Asabar

An wallafa

Ɗan wasan Manchester United, Marcus Rashford ya tsallake rijiya da baya, sakamakon hatsarin mota da ya yi a daren ranar Asabar.

Lamarin ya faru ne, bayan da Rashford ya bar sansanin atisayen United da ke Carrigton a cikin motarsa kirar Rolls Royce.

'Yan wasan United sun koma sansaninsu a cikin babbar motar kungiyar, bayan tashi daga karawar da suka ci Burnley 1-0 a gasar Premier ranar Asabar.

Daga nan kowanne ɗan wasan ya shiga motarsa, domin komawa gida daga sansanin atisayen da suka ajiye abubuwan hawansu a harabar.

An wallafa hotunan hatsarin da ɗan kwallon tawagar Ingila ya yi da halin da motar ke ciki.

Rashford ya buga wasan da United ta doke Burnley 1-0 a Turf Moor - karon farko da ta yi nasara a wasa daga fafatawa huɗu baya.

United ta fara da cin Wolverhampton da Nottingham Forest, yayin da Tottenham da Arsenal da Brighton suka yi nasara a kan kungiyar Old Trafford.