Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yaƙe-yaƙen Wagner da haƙar man fetur da zinare a ƙasashen duniya
A ranar Laraba ne aka samu labarin mutuwar shugaban sojojin haya na Wagner, Yevgeny Prigozhin a wani hatsarin jirgin sama a kusa da birnin Moscow, kamar yada gwamnatin Rasha ta sanar.
Hatsarin dai, babu mutum ko ɗaya a cikin mutum goma da ke cikin jirgin da ya tsira, na zuwa ne kwana guda kafin cikar wata biyu da wani boren sojoji.
Boren da aka shafe tsawon kwana biyu tsakanin 23 zuwa 24 ga watan Yuni da mayaƙan Prigozhin suka yi, an riƙa ɗiga ayar tambaya a kan karfin sojojinsa da kuma ayyukan da suke gudanarwa a Turai da Gabas ta Tsakiya da kuma Afirka.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya yi nazari kan aikace-aikacen ƙungiyar Wagner a faɗin duniya.
Ukraine
An tura mayaƙan Wagner ƙasar Ukraine, lokacin da sojojin Rasha suka ƙaddamar da mamaye cikin watan Fabrairun 2022, kuma lokacin bazara a bara sun sanar da shirinsu na ɗaukan dubban fursunoni da za su yi musu yaƙi.
A watan Disamban bara, lokacin da suka jagorancin yaƙin Bakhmut, hukumomin leƙen asirin Amurka ta ƙiyasta cewa Wagner ta ɗauki fursunoni dubu 40 domin amfani da su a yaƙin Ukraine.
Shugabannin Wagner sun yi iƙirarin zama ƙashin bayan nasarar ƙwace Bakhmut, tare da kushe ayyukan sojojin Rasha.
Kuma sun soki lamirin shugabancin ma'aikatar tsaro, suna zargin dakarun sojojin Rasha da dabaibaye ayyukansu da rashin ƙwarewa a yaƙin Ukraine.
Belarus
Prigozhin ya isa Belarus bayan janye niyyarsa ta boren sojoji, ƙarƙashin yarjejeniyar da suka cimma da Shugaba Alexander Lukashenko.
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce an yi wa mayaƙan tayi da kuma ba su zaɓin komawa can.
Hotunan da aka ɗauka ta tauraron ɗan'adam na sansanin sojoji a kusa da Asipovichi, da ke kudu maso gabashin Minsk, lokacin da kafofin yaɗa labaran Rasha suka ruwaito ƙungiyar za ta kaddamar da kanta, tare da nuna sabbin gine-gine da kuma ci gaban da suke samu ta fannin kayan yaƙi.
Amma a hukumance, tun bayan sanar da yarjejeniyar Belarus, da ta ƙunshi ba shi tsaro, Prigozhin ya kasance yana yawo ba tare da wata fargabar tsaro ba a cikin Rasha.
Syria
Jami'an Rasha sun ƙaddamar da ayyukan soji a Syria cikin shekara ta 2015 don mara baya ga Shugaba Bashar al-Assad da ke fuskantar hamɓararwa daga 'yan tawaye.
Gwamnatin Moscow ta tura sojojinta daga sansanin Hmeimem da ke Syria tare da amfani da sojojin haya irinsu Wagner don gudanar da wasu ayyuka, ɗaruruwa dai sun rasu a hannun Amurka cikin shekara ta 2018.
Ƙungiyar ta ƙwace iko da yankin al-Shaer mai arziƙin man fetur, kuma jami'an Ƙasashen Yamma sun ce su ne ke aiki da Evro Polis, kamfanin da ke samun kashi 25 cikin 100 na filayen man fetur da ke Syria.
Wagner ya ɗauki tsoffin 'yan tawayen Syria haya a yankunan Assad da suka ƙwace, inda suka riƙa amfani da su a yaƙin Libya daga 2019, yayin da sansanin sojin Hmeimin ya kasance wani yanki da ake kai-komo a tsakanin Rasha da Libya.
Amma ayyukansu a Syria ya koma Rasha cikin gaggawa bayan ƙoƙarin kifar da gwamnati a watan Yuni, inda aka mayar da galibin mayaƙansu ma'aikatar tsaro da ke Moscow.
Libya
Wagner ta shiga Libya a 2019 domin taimaka wa kwamanda Khalifa Haftar a yaƙin da yake yi a Tripoli domin fatatakar gwamnatin da ƙasashen duniya suka amince da ita.
Ma'aikatar tsaron Amurka ta ce a 2020 goyon bayan da mayaƙan Wagner suka riƙa bai wa Haftar, Hadaddiyar Daular Larabawa ce ta ɗauki nauyi, ta nuna musu goyon baya tare da Rasha da Masar.
UAE ba ta ce uffan ba lokacin da aka tuntuɓe ta domin tsokaci, a watan Yunin wannan shekarar lokacin da aka riƙa alaƙanta mayakan Wagner da wannan batu.
Sashen sa ido na Majalisar Dinkun Duniya ya ruwaito a 2020 cewa Wagner ta tura mayaƙa 1,200 zuwa Libya, sannan sojojin Amurka da ke ayyukansu a Afirka sun ce jirgin yaƙin Rasha sun riƙa jigilar mayaƙan Wagner a can.
Wagner ce ke iko da na'urorin kare hare-hare ta sama da kuma jiragen yaƙi daga sansanin Jufra na kudancin Tripoli, inda wasu jiragen ke isa daga Hmeimim inda Rasha ke da sansani.
Da kuma shigar da mayaƙa daga Syria a matsayin sojin haya, Wagner ta riƙa aiki da mayaƙan ne ƙetare daga Sudan da Chadi da wasu sassa.
Duk da yake, hare-haren Haftar sun kawo ƙarshe ba tare da nasara ba a 2020 bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.
Wagner ta ci gaba da zama a Libya inda take ayyuka a Jufra da sauran sansanoni na kudanci da gabashi inda masu bincike ke cewa suna amfani da damar wajen bazuwa a Afirka.
Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
Duk da ɗumbin arzikinsu na ma'adinai, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na cikin ƙasashe mafiya talauci a duniya.
Mayakan Rasha ciki har da Wagner sun shiga tsakani ta hanyar taimaka wa gwamnati wajen shawo kan yaƙin basasar ƙasar wanda aka fara tun a 2012.
Jakadan Rasha a Jamhuruyar Afirka ta Tsakiya, a wata tattaunawa da aka yi da shi ta kafar yaɗa labaran RIA, a watan Fabrairu ya shaida cewa, akwai dakarunsu 1,890 a ƙasar.
Masu sharhi na cewa Wagner sun karɓi bayanai da iko da mahaƙar zinaren ƙasar.
Amurka ta sanya takunkumi ga wani kamfanin na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kuma ɗaya daga cikin kamfanonin UAE da Washington ta ce suna taimaka wa Wagner da kuɗi ta hanyar kasuwancin zinare ta haramtacciyar hanya.
Mali
Kasashen Rasha da Mali sun ce sojojin hayan Rasha ba mayaƙa ba ne na dindindin, amma ana iya bayyana su da ƙwararru da ke taimaka wa sojoji wajen yaƙi da masu iƙirarin jihadi da suka daɗe suna adabar yankuna.
Sojojin Mali sun ƙwace mulkin ƙasar a 2021 yayin wani juyin mulki, da shigar mayaƙan Wagner bayan buƙatar sojojin Faransa su fice daga ƙasar.
Gwamnati na tattaunawa kai tsaye da Wagner, inda suke biyansu kusan dala miliyan 10.8 kuɗin ayyukansu, a cewar rahoton Reuters na 2021.
An zargi mayaƙan Wagner da hannu a abin da ya faru a Moura a shekarar da ta gabata, inda dakarun yanki da mayaƙan da ake zargi na Rasha suka kashe ɗaruruwan fararen hula.
Sudan
Kasashen Yamma da jami'an diflomasiyya sun ce Wagner na da hannu a satar zinare, da yaɗa labaran bogi da ingiza rikicin siyasa a Sudan yayin da Rasha ke ƙoƙarin bitar abubuwan da suka faru a baya da kuma bayan kifar da Omar al-Bashir a 2019.
Yayin da Moscow ke da alaƙa da ɓangarorin da ke rikici da juna a yaƙin Sudan da aka fara tun Afrilu, ana zargin Wagner na da kyakyawar alaƙa da sojojin RSF, maimakon sojin gwamnati na Sudan.
Wagner ta musanta cewa tana ayyuka a Sudan, Suna cewa kusan shekara biyu babu sojojnsu a ƙasar, sannan babu ruwansu a yaƙin da ake yi a ƙasar.
A watan Mayu, Amurka ta zargi Wagner da bai wa RSF makamai, wanda hakan ya tsawaita yaƙin da ake yi.