Kididdiga kan yadda aka buga Premier League ta 2022/23

An wallafa

An kammala gasar Premier League ta kakar 2022–23, wadda Manchester City ta lashe kofin bana.

An fara bikin bude makon farko ranar 5 ga watan Agustan 2022, sannan aka kammala ranar 28 ga watan Mayun 2023.

An yi karawa 380 da cin kwallo 1,084 daga ciki Erling Haarling ya zura 36 a raga, ba wanda ke gabansa a wannan bajintar.

Gajerin batutuwan da Mohammed Abdu ya hada kan gasar ta Premier:

Kungiyar ta da lashe Premier League:

Manchester City ce ta dauki kofin bana da maki 89, wadda ta lashe na uku a jere na biyar a kaka shida, amma na bakwai jimilla.

Kungiyoyin ukun da suka bar Premier League:

  • Leicester City
  • Leeds United
  • Southampton

Wadanda za su buga Champions League a badi:

  • Manchester City
  • Arsenal
  • Manchester United
  • Newcastle United

Wadanda za su wakilci Ingila a Europa League:

  • Liverpool
  • Brighton & Hove Albion

Wadda za ta kara a Europa Conference League

  • Aston Villa

Fitatcen mai tsaron raga:

David de Gea na Manchester United

(Wasa 17 kwallo bai shiga ragarsa ba)

Wasan da kungiyar gida ta ci kwallaye da yawa:

Liverpool 9–0 Bournemouth

(Ranar 27 ga watan Agustan 2022)

Karawar da aka ci kungiyar da ke gida kwallaye da yawa:

Leeds United 1–6 Liverpool

(Ranar 17 ga watan Afirilun 2023)

Wasannin da aka zura kwallaye da yawa a raga:

Liverpool 9–0 Bournemouth

(Ranar 27 ga watan Agustan 2022)

Manchester City 6–3 Manchester United

(Ranar 2 ga watan Oktoban 2022)

Kungiyar da ta jere cin wasanni:

Manchester City karawa 12

Wadda ta yi wasa da yawa ba tare da an doke ta ba:

Newcastle United fafatawa 17

Kungiyar da ta yi karawa da yawa ba tare da yin nasara ba:

Southampton wasa 13

Wadda ta yi rashin nasara da yawa a jere:

Leicester City wadda aka ci fafatawa shida a jere

Southampton wadda aka doke karo shida a jere