Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An bai wa Bellingham jan kati a wasan Sevilla a La Liga
An bai wa Jude Bellingham jan kati a wasan da Real Madrid ta ɓarar da damar bayar da tazarar maki huɗu a teburin La Liga, bayan da ta tashi 1-1 a gidan Osasuna.
Real Madrid ta je Osasuna, domin buga karawar mako na 24 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
An kori ɗan wasan tawagar Ingila kai tsaye a minti na 39, sakamakon keta da faɗin kalamai marasa daɗi ga alkalin wasa, Jose Luis Munuera Montero.
Wasan da a baya aka bai wa Bellingham jan kati a Real shi ne a Valencia da suka tashi 2-2 a Maris ɗin 2024, saboda ƙorafi da ya yi ga rafli.
Ɗan wasan tawagar Faransa, Kylian Mbappe shi ne ya ci wa Real ƙwallon, kuma na 17 da ya zura a raga a babbar gasar tamaula ta Sifaniya ta bana.
Osasuna ta farke a bugun fenariti a minti na 58 ta hannun Ante Budimir, bayan da Eduardo Camavinga ya yi keta a cikin da'ira ta 16.
Idan Atletico Madrid, wadda ke karbar bakuncin Celta Vigo ranar Asabar ta ci karawar za ta hau kan Real Madrid a teburin La Liga.
Haka kuma idan har Barcelona ta yi nasara a kan Rayo Vallecano ranar Litinin za ta iya hau kan Real Madrid.
Kafin wasan Atletico Madrid ranar Asabar, Real Madrid tana ta ɗayan teburi da maki 51, Atletico ta biyu tana da maki 49 da Barcelona mai maki 48 ta ukun teburi.