Europa League: Juventus da Sporting

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar Sporting Club ta ziyarci birnin Turin, domin karawa da Juventus a zagayen quarter-finals a Europa League ranar Alhamis
Wasa na uku da za su kece raini a tsakaninsu, bayan da suka fafata sau biyu a Champions League a kakar 2017/18
Wasa biyu da suka kara a tsakaninsu:
Champions League Talata 31 ga watan Oktoban 2017
- Sporting 1 - 1 Juventus
Champions League Laraba 18 ga watan Oktoban 2017
- Juventus 2 - 1 Sporting
Juventus ba a doke ta ba wasa 14 daga 21 da ta fuskanci kungiyoyin Portugal a gasar zakarun Turai da lashe 11 daga ciki.
Na karshe daga ciki shine da Porto a Champions League zagayen 'yan 16 a kakar 2020/21.
Sporting ta kasa nasara a karawa 15 da ta buga a waje da shan kashi 11 a hannun kungiyoyin Italiya a gasar zakarun Turai.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Duk da cewar Sporting ce ta fitar da Arsenal a Europa a bana, kocin kungiyar, Ruben Amorim ya ce ''Ba ma cikin wadanda ake hasashen za mu lashe kofin bana.
Ya kara da cewar ''Ina iya kokarin ganin Sporting ta taka rawar gani a bana, amma bama cikin zakakuren dake sawun masu cin kofin Europa League a yanzu - nan gaba za mu shiga sahun manyan kungiyoyin.''
Sporting tana ta hudu a teburin gasar tamaula ta Portugal da tazarar maki 14 tsakaninta da Benfica mai jan ragamar kakar nan.
Ita kuwa Juventus tana ta bakwai a teburin Serie A, ba ta jerin gurbin wadanda za su wakilci Italiya a badi a gasar zakarun Turai a wannan matakin.
An kwashe mata maki 15 daga wanda Juventus ta hada a bana, bayan da aka same ta da laifin karya ka'idar kasuwanci da kungiyar ta yi.
Saboda hada dukkan kungiyoyin biyun sun dogara ga lashe Europa League na bana, domin su samu shiga gasar zakarun Turai ta badi cikin ruwan sanyi.
Ranar 20 ga watan Afirilu, Juventus za ta ziyarci Sporting, domin buga wasa na biyu a Portugal.











