Yadda mutum-mutumi ke aiki a gidan abinci da 'yarjarida mai sukar gwamnati

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Zaɓɓaɓun ƙayatattun hotunan Afirka da na ƴan nahiyar a wasu sassan duniya cikin makon da ya gabata

Ƴan takarar sarauniyar kyau ta Kenya a lokacin da suke shiryawa a bayan fage a ranar Juma'a.

Ƴan kallo a wajen taron fitar da sarauniyar kyau ta Kenya ke kirari ga gwanayensu.

A lokacin da mai tallar kayan ƙawa ke tallata kayan ɗan Najeriya Adebayo Oke-lawal a wajen bikin nuna kayan ƙawa a Birtaniya.

Yadda shahararriyar ƴar wasan kwandon Mali, Maimouna Haidara ta ƙawata gashinta a wajen wasan da suka buga da Venezuela a Mexico.

Giwa mai shekara 42 da aka mayar a wani gidan kayan tarihi na lardin Limpopo da ke Afirka ta Kudu a ranar Laraba.

Wata Kwastoma kenan a lokacin da take godiya ga butun-butumin da ya kai mata abinci a gidan abincin butun-butumi a Nairobi a ranar Alhamis.

Dricus Du Plessis na Afirka ta Kudu tare da Israel Adesanya na Najeriya, rungume da juna bayan kammala fafatawa a wasan dambe na ajin matsakaita ranar Lahadi, bayan Dricus ya lashe fafatawar.

Ƴan ƙasar Gabon kenan a lokacin d asuke ɗaga tutar ƙasar a yayin faratin tunawa da samun ƴancin kai a babban birnin ƙasar Libreville a ranar Asabar.

Yar jarida kuma mai sukar gwamnatin Burundi, Floriane Irangabiye a lokacin da take godewa tawagar lauyoyin da suka roƙi shugaban ƙasar ya sako ta daga gidan yari, bayan sakinta a ranar Juma'a.

Wasu kenan da suke amfani da kwale-kwale domin zagayawa a babban birnin ƙasar Chadi, N'Djamena inda aka samu ambaliyar da ta yi sanadiyar rushewar gidaje sama da 16,000.

Wata uwa a gabashin Kongo, Justine Munguiko riƙe da yarinyarta da aka yi wa maganin cutar ƙyandar biri.

An karrama tauraruwar fina-finai kuma mawaƙiyar Afirka ta Kudu a Johannesburg, Abigail Kubeka a matsayin wadda ta cika shekara 67 cikin msana'antar.

Mawaƙan zamani masu salon rap Wadagliz da aka yi amfani da sautinsu a yayin zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a Kenya.