Yadda mace za ta gane ruwa mai cutarwa da ke fita daga al'aurarta
Wannan shiri ci gaban na wancan makon ne da ya gabata.
Cutar sanyi ta Candidiasis na daya daga cikin cututtukan da ke janyo kaikayi a al’aurar mata, musamman ma a tsakanin mata masu ciki.Sai dai rashin tsafta na daga cikin manyan abubuwan da masana a fannin kiwon lafiya suka ce yana janyo cutar sanyin.Wasu karin dalilan da ke janyo wa mata samun cutar sanyin ta Candida, sun hada da ciwon suga da yin amfani da magungunan kashe kwayoyin cuta fiye da kima da wasu magungunan hana daukar ciki da samun juna biyu.Haka zalika wasu daga cikin alamomin cutar su ne kaikayin gaba da kuraje da zafi lokacin fitsari da zafi lokacin saduwa da zafi a mara.Yayin da hanyoyin kauce wa cutar sun hada da tsafta da sanya wando mai laushi na auduga da daina maganin kashe kwayoyin cuta sai abin da likita ya ya rubuta. Cutar sanyi wadda ake kira yeast infection ko candidiasis da turanci ingishi, cut ace da ke addabar miliyoyin mata a duniya.Kuma a cewar hukumar yaki da cututtuka ta Amurka, CDC, cutar sanyin cuta ce mai sauki, sai dai ga wasu matan ta kan zo musu da tsanani ta yadda ta kan janyo musu kunburi da tsagu a gabansu.Haka kuma wurin ya kan sauya launi ya yi ja.Alkaluman hukumar yaki da cututtuka ta Amurka ta ce akwai mata 1. 4 miliyan da ke zuwa asibiti neman maganin cutar sanyi ta candidiasis akowace shekara.