"Sai bayan AFCON za mu tantance matsayin Peseiro"

Bayanan bidiyo, Ibrahim Musa Gusau ya yi bayani dangane da yadda suke bai wa yaransu horo
"Sai bayan AFCON za mu tantance matsayin Peseiro"
An wallafa

Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Najeriya, Ibrahim Musa Gusau ya ce babu wata yarjejeniya da ke tsakaninsu da kocin tawagar Najeriya a gasar cin kofin Afirka ta AFCON da ake yi a kasar Ivory Coast, Peseiro Wary bayan kammala gasar.

Ibrahim Gusau ya kara da cewa "abin farin ciki yanzu shi ne duk wasu basuka da yake bin mun samu daga gwamnatin tarayya za a biya shi."

Sai dai ya ce za su iya daukar koci ne daga wace irin kasa ta duniya ba lallai sai dan Najeriya ba.

"Abin da ake so shi ne a samu kwararre wanda zai samar da sakamako mai kyau".