Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda aka rufe kasuwar ƴan canji a Abuja
Yadda aka rufe kasuwar ƴan canji a Abuja
An wallafa
Ƴan kasuwar canji da ke Abuja sun ce sun rufe kasuwar musayar kuɗin ƙasar waje da ke babban birnin ƙasar Abuja.
Shugaban ƙungiyar ƴan kasuwar Abdullahi Abubakar Dauran ya shaida wa BBC cewa sun ɗauki matakin ne sakamakon yadda gwamnati ta buƙaci hakan daga gare su.
A baya-bayan nan dai jami'an tsaron ƙasar sun yi ta kai samame kasuwar a wani yunƙuri na daƙile tashin farashin dala a ƙasar.
Shugaban ƴan kasuwar ya ce a ɓangarensu sun yi biyayya ga umarnin gwamnati, domin yana da yaƙinin cewa gwamnatin ta yi hakan ne da kyakkyawar manufa.