Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sudan: 'Dan'adam ba shi da sauran daraja a El-Fasher'
- Marubuci, Mohamed Osman
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic
- An wallafa
**Gargaɗi: Wannan labari na ɗauke da abubuwa masu tayar da hankali
Saadia 'yar asalin El-Fashe(ba sunanta ne na gaskiya ba) tana ziyara a gidan makwabtanta a lokacin da wani hari ya faɗa kan gidanta.
Nan take ta ruga da gudu ta nufi gidan nata, zuwanta ke da wuta ta iske bom ya faɗa harabar gidanta, inda ya kashe duka 'ya'yanta biyu.
Kwanaki kaɗan da suka gabata ne mummunan faɗa ya ɓarke tsakanin sojojin gwamnati da dakarun RSF a birnin da aka yi wa ƙawanya.
Cikin wani saƙon murya ta shaida wa BBC cewa a lokacin da ta koma gidanta ta kasa gaskata abin da idanunta suka gani.
“Abin tashi hankali ne, na samu 'ya'yana Samar da Sahar bom ya yi filla-filla da su a tsakar gidana, a kusa da su kuma ga mahaifinsu yana sharɓar kuka,” in ji ta.
Labarin wata mahaifiya
“Ina ma a ce ni ce na mutu ba 'ya'yana ba."
Kafin ta gama warwarewa daga wannan tashin hankali da ta shiga, sai ta ji wani kururuwa daga makwabta.
Ashe bom ɗin da ya faɗa gidanta ya shafi gidan makwabtan nasu tare da kashe ƙaramin ɗansu mai suna Riad.
Saadia da mijinta sun yanke shawarar barin gidan nasu, domin komawa sansanin 'yan gudun hijira da ke unguwarsu.
Saadia ta ce ta samu tarba mai kyau a sansanin, inda a nan ne kuma ta fara samun nutsuwa.
To sai dai kwanciyar hankalin da ta fara samu bai ɗore ba, sakamakon hare-haren jiragen saman sojin ƙasar da makaman atilare daga mayaƙan RSF.
"Kan haka ne na yanke shawarar barin El-Fasher ni da ƙaramin ɗana da ya rage min, shi kuwa mijina ya ci gaba da zama a can sakamakon fargabar kamashi da yake yi,” in ji ta.
Ficewa daga el-Fasher ba abu ne mai sauƙi ba, abu ne mai cike da hatsari, to amma Saadia ba ta da wani zaɓi illa ta fice daga birnin.
"Tun da asuba muka fice daga birnin, a cikin wata ƙaramar mota tare da wasu iyalai da dama ciki har da ƙananan yara da tsofaffi. Kuma abin daɗin shi ne babu wata matsala da muka ci karo da ita a hanyarmu sai ɗan abin da ba a rasa ba.''
Ta ce bayan tafiya ta sa'o'i masu yawa a kan hanyar da ke cike da shingayen bincike, a ƙarshe sun isa birnin Mellit.
Ɗaya daga cikin dalilan da suka sa take tunanin sun wuce ba tare da wata matsala ba, shi ne kasancewar babu namiji ko ɗaya a motar, kuma direban na biyan kuɗi ga sojojin da suka samu a kowane shingen bincike.
“Kasancewar da asuba muka fita wasu ma shingayen binciken babu kowa, waɗanda muka samu kuma matasa kawai suke dubawa a cikin mota ko makami,” in ji ta.
Ana binne gawarwaki ba tare da likkafani ba
El-Fasher shi kaɗai ne birnin da ke ƙarƙashin ikon sojoji a ilahirn yankin Darfur, kuma birni ne mai matuƙar muhimmanci a yaƙin da ake yi.
Idan birnin ya kuɓuce wa sojoji, ilahirin yankin Darfur zai koma ƙarƙashin ikon jagoran dakarun RSF, Mohamed Hamdan Dagalo, da aka fi sani da Hemedti.
Shi kaɗai ne babban birnin da za a iya shigarsa daga arewacin Sudan, kuma shi kaɗai ne wurin da motocin jin kai ke zuwa idan sun taso daga tashar jiragen ruwa ta jihar Port Sudan da ke kusa da tekun Maliya.
Wannan sabon rikicin da ya ɓarke tsakanin ɓangarorin biyu ya raba birnin da sauran yankunan duniya, musamman bayan katsewar sadarwa.
Sadiq Hassan, babban sakataren ƙungiyar lauyoyin yankin Darfur ya bayyana takaicinsa kan halin da ake ciki a birnin.
A yayin da hukumomi ke ƙiyasta mutanen da suka mutu a rikicin da 150, ƙungiyarsa ta yi ƙiyasin cewa adadin ka iya ninkawa.
Wasu mutane kan ''binne gawarwaki ba tare da likkafani ba, ko ba tare da kai su asibiti ba'', in ji Dakta Hassan.
"Dan adam ba shi da sauran daraja a nan," in ji shi. Ana yi wa fararen hula “kisan gilla ba tare da wani dalili ba, mayaƙa na kai wa fararen hula muggan hare-hare."
Hassan ya ce duka ɓangarorin biyu na amfani da fyaɗe a matsayin makami a yaƙin.
"Mun samu rahotonni da dama na kisan kai da fyaɗe da cin zarafi na lalata."
Ya ce akwai 'yan gudun hijira da dama da suka isa birnin daga sassan yankin Darfur.
Suna rayuwa cikin mawuyacin hali, saboda ƙarancin abinci da ruwan sha, bayan wawashe gidajen ajiyar abinci na Majalisar Dinkin Duniya da na sauran ƙungiyoyi, kamar yadda ya yi bayani.
Harin bom kan asibiti
Likitoci a ɗaya daga cikin asibitocin da ke aiki a El-Fasher sun ce an tilasta musu rufe asibitin bayan harin da aka kai masa.
Ƙungiyar Likitoci da Duniya MSF, ce ke tallafa wa asibitin - wanda ake gani shi kaɗai ne ya rage a birnin El-Fasher da fararen hula ke samun magani.
Cikin kwanaki da suka gabata an samu rahotonnin hare-hare a kan asibitin, lamarin da ya haddasa raunuka da mace-mace.
Dakatar da ayyuka a asibitin, zai kasance babban koma-baya ga al'ummar El-Fasher, kasancewar shi kaɗai ne asibitin da ke maganin raunuka.
Shi ne “kawai asibitin da ke da kayan aikin da zai iya yi wa mutane da dama magani, kuma ɗaya daga cikin asibitoci biyu da ake iya yin tiyata a birnin,'' in ji ƙungiyar MSF, wadda ta ce fiye da masu raunuka 1,300 ne aka yi wa magani a asibitin a watan da ya gabata.
Ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ya tabbatar da cewa duka ɓangarorin suna kai hari kan fararen hula.
"Mafi yawan yankunan El-Fasher ba su da wutar lantarki da ruwan sha, kuma mutane ƙalilan ne ke samun muhimman abubuwan more rayuwa ciki har da abinci da kiwon lafiya," in ji wani jami'in ofishin, Clementine Salami.