Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaben Italiya: Meloni mai tsattsauran ra'ayin rikau ta fara sansano nasara a kasar da kawuna suka rabu
Daga Mark Lowen Wakilin BBC a Rome
Yayin da lokacin zabe ke kara gabatowa, a kasuwar Ballaro da ke Sicily, babban birbin Palermo, a iya cewa ba batun siyasar ne a gabansu ba. 'Yan kasuwa na ta kiran kwastomomi, yayin da wasu ke yin fale-fale da nau'o'in naman ruwa, wasu kuma na dafa wani abincin gargajiya mai suna: arancini ko dunkulalliyar shinkafa da aka cura cikin nama. Sai dai mutanen ba su damu da wani batu na siyasa ba. Wasu na ta shawagi a rumfunan kasuwar, yawancin wadanda muka zanta da su, sun ce ba za su jefa kuri'a a zaben da ke tafe a ranar Asabar ba.
Kalmomin yaudara, cin amana da handama su ne yawancin mutanen ke cewa suka janyo ba sa sha'awar yin zabe. Da take bare lemon zaki da ruman a kofar kantin sayar da Gahwa, Sonia Capizza ta sha bamban da sauran: a baya ta sha alwashin daina zuwa zabe, amma a wannan karon lamarin ya sauya. "Na fara ganin lamura na sauyawa, alamu sun bayyana a kan Giorgia Melano", in ji ta, tana magana ne a kan shugabar jam'iyyar Brothers of Italy, mai tsattsauran ra'ayin rikau, da ke sahun gaba a kuri'ar jin ra'ayin jama'a. "Tana jan hankalina saboda ita mace ce, uwa ce, tana da nutsuwa da kwarjini".
A zaben shekarar 2018, jam'iyyar Meloni ta samu kashi hudu kacal na kuri'u, yayin da dan takarar jam'iyyar Five Star Movement, ya samu kashi 50 na kuri'un da aka kada a nan. Shekaru hudu kenan, kuma jam'iyyar Brothers of Italy ta sake yunkurowa, inda ta shiga kawancen masu ra'ayin rikau, sun fara tunanin yin nasara. Memis Meloni, mai shekara 45, ka iya zama firaiminista mace ta farko a kasar Italiya, kuma mace ta farko shugabar jam'iyyar masu ra'ayin rikau, tun bayan Benito Mussolini. Yanki mafi talauci a kudancin Italiya, ya samu tagomashi kuma a zaben da ke tafe za su sake zabar jamiyyar Fice Star ne.
Amma ga wasu kamar Mis Capizzi na da ra'ayin marawa Meloni baya. "Da halin da ake ciki, mutane na zaman kashe wando a gida, ba sa aikin komai, kamata ya yi gwamnati ta samar da ayyukan yi," in ji mai kantin sayar da Gahwa.
Ko a wajen birnin Palermo, ba ta sauya zani ba, misali a yankin Zen da ke fama da rashin aikin yi. Yanki ne mafi rashin ci gaba a Turai, inda rashin aikin yi ya kai kashi 50 cikin 100, sannan kashi 80 na matasa zaman kashe wando kawai suke yi. Mun zanta da wasu maza biyu, Domenico Finnochio da Pier Gambino, suna zaune a wani takurarren rukunin gidaje, gilasan tagogin sun farfashe. A gefen wurin akwai wasu konannun motoci, da himilin bola. Dukkan mazan sun zabi jam'iyyar Five Star a zaben da ya wuce, amma yanzu sun ce Mis Meloni za su jefawa kuri'arsu. "Muna son ganin an tsaftace yankin mu, yadda ba za mu dinga fuskantar barazana da daddare ba," in ji Domenico.
"Babu ta inda za ka kwashe bolar nan, saboda Beraye ke dabdala a wurin." Shi kuwa piero cewa ya yi: "Muna fatan Five Star za ta kawo mana sauyi, amma duka surutu suka iya babu aiki, kuma mu na fama da rahsin aikin yi.
"Muna ganin kamar an mayar da mu saniyar ware, fatanmu dai shi ne Allah ya sa Meloni ta kawo mana sauyi da ci gaba."
Sai dai kawunan yan Italiya a rarrabe suke. A birnin Modena na kasar, gefen tituna cike ya ke da allon tallan kayan taba-ka-lashe, da kwalam, misali irin abincin gargajiya mai suna totellini da ake cusa nama cikin kwarorin taliya makaroni, su ake ta rabawa a wurin bikin kalankuwa na Unita da ke hada kan jamiyyar masu ra'ayin rikau.
Batun siyasa a wannan wuri, ya sha banban da wanda ake gani a yankin da Meloni ta ke da rinjaye.
Batutuwa ake tattaunawa akai da suka shafi muhawara kan yakin Ukraine, da ilimi, ba su ne a gabasu ba, kawai abin da suke nema shi ne kada a bar Italiya ta fada hannun masu ra'ayin rikau. "Na damu matuka kan Mis Giorgio Meloni, ita ce macen da ta fi kowacce rashin tsinkaye," in ji Barbara Rosi, manajar kasuwanci a wani kamfani da ta zo wurin cin abinci tare da yan gidansu. "Ina tsoron kar ta take mana bakki da yancin da muke da shi, musamman batun zubda ciki. Ina mata kallon wakiliyar zamanin da muka sha wuya, hannun shugaban da ke mulkin mulaka'u a kanmu sai abin da suka ba mu umarnin aikatawa, kuma abin da ta ke son sake dawo da shi kenan a Italiya," in ji Rosi.
Shugaban jam'iyyar Brotgwrs of Italy, bai amince da salon mulkin danniya ba, a baya-bayan nan ya kira tsarin da kuskureb da magabata suka yi kuma lokacin ya shude. Italiyawa da dama na ganin tsarin jam'iyyar Mis Meloni na daga cikin abin da ke darsa shakku a zukatan masu zabe, ka da su gujewa Gara su samu Zago a daki. Wani bidiyo da aka yada a bara, ya nuna wasu shugabannin jam'iyyar na jinjinawa salon mulkin danniya. Abun da ya bayyana karara shi ne manufofin Meloni na siyasa da ake damuwa akai shi ne yadda ta ke fitowa karara ta bayyana ra'ayin ta kan batutuwa da dama.
Misali kan batun masu auren jinsi da ta nuna kin amincewa da shi. "Ina goton bayan iyalai, amma ban da iyakai masu auren jinsi daya," abin da ta fada kenan lokacin gangamin yakin neman zabe a Sicily. Wannan ya darsa tsoro a zukatan, Christian De Florio da kuma Carlo Tumino, iyayen wasu yan biyu masu shekaru 4, da suka same su ta hanyar wata Ba'amurkiya da ta amince ta dauki cikin.
Lokacin da yarab ke dakin girki, sun shaida min abinda suke gani kan manufar Mis Meloni. " So take ta shafe babin iyalai kamar mu". "Ta na amfani da dabarun gano makiya," in ji Carlo.
"Masu auren jinsi kamar mu, da masu sauya halittarsu, da 'yan ci-rani su ne makiya. Ba na son yadda ta ke nunawa da bayyana raayinta karara.
Kullum cikin fushi ta ke, musamman ga mutanen da ba ra'ayinsu daya ba.
Ina ganin kamata ya yi kowa ya yi irin rayuwar da ya ke muradi, wanna ita ce dimokuradiyya".