Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko taron-dangin ƴan siyasa zai iya kawar da Tinubu a 2027?
Da alama 'yan siyasa daga arewaci da kudancin Najeriya suna ta hadin gwiwa tare da kakkafa kungiyoyi da dama, a wani yunkuri na kwace mulki daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC a zaben kasar na 2027.
Wannan na zuwa daidai lokacin da mafi rinjayen al'ummar Najeriya ke ta faman kukan tsadar rayuwa da tsawwalar haraje-haraje da sauran matsaloli.
Wasu jiga-jigan 'yan siyasa masu bambance-bambance iri-iri daga sassa daban-daban na kasar, suna nan suna ta haba-maza wajen hada kai da tattaunawa da juna domin kawo sauyin gwamnati a kuri'ance.
Ya zuwa yanzu kuma akwai kungiyoyi irin LND ta su tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Malam Ibrahim Shekarau, da kuma wata tattaunawa da ake yi a karkashin jam'iyyar SDP, da wata maja da wasu fitattun 'yan siyasa irin su Rauf Aregbesola ke kokarin yi a jam'iyyance da dai sauran su.
Sai dai masana irin su Farfesa Abubakar Umar Kari, masanin kimiyyar siyasa da ke jami'ar Abuja, ya ce wannan ba bakon abu ba ne hasali ma an ga hakan a lokuta da dama.
''Ai mun ga hakan a jamhuriya ta biyu da ta uku da wadda muke ciki a halin yanzu, daga lokaci zuwa lokaci ana irin wannan hadaka, muna ganin taron dangin da wadanda ba su da iko ke yi domin tunkarar jam'iyyar da ta ke mulki. Sai dai tarihi ya nuna cewa nasarar hadakar ya danganta da su wanene suka shirya tafiyar.
Yawancin lokaci tafiyar masu hadakar tana cike da gargada, da nisa cike take da abubuwa da dama. Na farko dai akan samu banbancin akida, da manufa sannan yawancin jiga-jigan tafiyar manufarsu daya ce wato kowa so yake ya rike madafun iko. To wannan dalilin na daga cikin dalilan da ke dasa shakku kan nasarar tafiyar hadaka irin wannan,'' in ji Farfesa Kari.
Duk wata hadaka da za a yi, don kawar da gwamnati APC daga karagar mulki a zaben shekara ta 2027, na tattare da babban kalubale, in ji Farfesa Abubakar Umar Kari.
A cewarsa APC za ta yi komai mai yiwuwa da kulle-kulle su tabbatar sun hana wannan tafiya, za su yi amfani da 'yan cikin gida na hadakar jam'iyyun domin wargaza tafiyar baki daya. Saboda sun san matukar sukai sake hadakar ta kafu to tabbas ja da su ba abu ne mai yiwuwa ba, dan haka komai za su yi sai sun cimma nasarar raba tafiyar 'yan majar.
Masanin kimiyyar siyasar dai yana ganin ko da hakar 'yan siyasar na bangaren hamayya za ta cim ma ruwa, sai sun kawar da kalubalen da ke kan hanyar tafiyar tasu, kuma su yi tsayuwar daka tare da fuskantar alkibla guda don cim ma manufar tasu.
A baya dai an ga alfanun irin wannan haɗaka, inda a shekarar 2015 haɗakar jam'iyyun da suka dunƙule cikin jam'iyyar APC suka yi nasara, lamarin ya bai wa tsohon shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari damar lashe zaɓen shekarar.