Zanga-zangar nuna adawa da gwamnan Babban Bankin Najeriya
Zanga-zangar nuna adawa da gwamnan Babban Bankin Najeriya
An wallafa
A ranar Laraba ne 3 ga watan Mayu, gomman 'yan Najeriya suka gudanar da wata zanga-zangar nuna adawa da gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele.
Masu zanga-zangar maza da mata, wasunsu ɗauke da allunan da aka yi rubuce-rubuce sun yi ƙorafi game da wahalhalun da suka ce canjin kuɗin da babban bankin ya yi a watannin baya-bayan nan, suka jefa su.
Sun dai yi kira a tuɓe Godwin Emefiele, sai dai hukumomin babban bankin ba su ce uffan ba lokacin da BBC ta tuntuɓe su don jin martanin da za su yi.



