Haji Malang: Wurin ibadar Sufaye da mabiya addinai ke jayayya a kansa a Mumbai

An wallafa

Wajen ibadar na Sufaye wanda Indiyawa mabiya addinai daban-daban ke yawan ziyarta ya dauki hankali ne a kwanan nan bayan da wani babban dan siyasa a kasar ta Indiya ya ce yana son ya ceto shi domin mallaka shi ga mabiya addinbin Hindu.

A kan haka ne wakiliyar BBC, Cherylann Mollan ta ziyarci wajen domin sanin abin da ke janyo takaddama a kai.

Da farko dai waje ne da ke kan tsauni wanda hawansa kadai ba karamin kokari ba ne. Matattakala 1,500 da aka sassara a jikin dutsen masu ibada ke hawa har su kai samansa, inda a can din kuma akwai kabarin wani wali na Sufaye, wanda ke dauke da tarihin da ake takaddama a kansa.

Wannan wajen ibada da ake kira da Haji Malang yana can kan tsauni ne kamar yadda muka fada a baya, a wajen birnin Mumbai a jihar Maharashtra, ta yammacin kasar.

An ce akwai kabari ko hubbaren wani Balarabe mai wa'azi wanda ya je Indiya sama da shekara 700 da ta wuce.

Kamar sauran wurare da dama na ibada a kasar ta Indiya shi ma wannan wuri ana yi masa kallon waje ne na hadin kai da mutunta addinin juna duk da cewa wuri ne kuma na takaddama ga addinai.

Lokacin da na ziyarci wurin na tarar mabiya addinin Hindu da kuma Musulmi na ajiye furanni da kuma wani farin kyalle da ke zaman wata alama ta girmamawa ga Sufaye a kan kabarin.

Mabiya sun yi imanin cewa duk abin da mutum ya roka in har ya kasance da zuciya mai tsarki to zai samu biyan bukata.

Hukumar da ke kula da wurin ta san wannan muhimmanci da mutunta addinin juna da mabiya addinan biyu suke yi, inda mutum biyu daga cikin amintattun hukumar da ke kula da shi Musulmi ne, duk kuma da cewa ainahin wadanda suke kula da wurin na gado sun fito ne daga Iyalan Brahmin mabiya addinin Hindu.

To amma a farkon watan nan ne babban Minista na jihar ta Maharashtra, Eknath Sambhaji Shinde ya taso da tsohuwar takaddama a wajen wani gangamin siyasa, inda ya ce a tarihi wajen na mabiya addinin Hindu ne kuma ya ce zai ceto shi domin tabbatar musu da shi.

Sai dai duk kokarin da BBC ta yi domin ji daga gare shi amma bai ce komai ba.

Ministan ya yi ikirarin ne a lokacin da ake ta takaddama a Indiya cewa wasu fitattun masallatai da wurare masu muhimmanci na Musulmi an gina su ne a wuraren da aka rushe wuraren ibada na Hindu daruruwan shekaru da suka gabata.

A shekarun 1980 mutumin da ya kasance ubangida na siyasa ga Mista Shinde, Anand Dghe ya jagoranci wata fafutuka ta neman sake kwato wannan wuri na ibada domin mallaka shi kacokan ga mabiya Hindu.

A shekarar 1996 an ce ya jagoranci ma'aikata 20,000 daga jam'iyyar Shiv Sena, inda suka gudanar da wata ibada ta Hindu.

Tun daga wannan lokacin ne mabiya addinin Hindu masu tsattsauran ra'ayi da ke kiran wurin da suna Malanggad, suke gudanar da wannan ibada a duk ranakun karshen wata, inda a wani lokaci lamarin ke haifar da hatsaniya tsakanin Musulmi da mutanen yankin.

To amma masu lura da al'amuran siyasa na ganin cewa matsayar Mista Shinde ba ta da alaka da addini kamar yadda take da siyasa.

Domin fafutukar Dighe a wancan lokacin ta kara masa farin jini a tsakanin mabiya addinin Hindu a jihar ta Maharashtra.

"Yanzu Mista Shinde na kokarin sanya kansa a matsayin mai ceton mabiya addinin Hindu a jihar Maharashtra in ji Prashant Dixit, wani tsohon dan jarida.

Nan gaba a wannan shekara ne baya ga babban zaben kasar ta Indiya, jihar ta Maharashtra - wadda ita ce mafi arzki a kasar za ta yi zaben majalisar dokokin jihar.

Samun goyon baya daga 'yan Hindu mafiya rinjaye abu ne mai muhimmanci sosai ga Mista Shinde, idan aka yi la'akari da matsayin siyasar jihar, in ji Mista Dixit.

Zabe a jihar Maharashtra galibi yana kasancewa ne gwagwagwa tsakanin bangarori hudu wato 'yan gargajiyar yankin da 'yan jam'iyyar mabiya Hindu ta kishin kasa, Shiv Shena da jam'iyyar Bharatiya Janata Party (BJP) da jam'iyyar masu tsaka-tsakin ra'ayi ta Nationalist Congress Party (NCP) da kuma ta Congress, inda kowane bangare ke samun kasonsa na magoya baya.

To amma Mista Shinde na fuskantar karin kalubale domin a shekarar 2022 shi da magoya bayansa sun sauya sheka daga jam'iyyarsu ta Shiv Shena.

Matakin ya kai ga kawar da gwamnatin hadakar jam'iyyu uku kuma wata hadakar ta Shiv Shena da Congress da NCP ta samar da wani sabon kawance da BJP domin samar da sabuwar gwamnati.

''To amma duk da cewa 'yan majalisa na iya sauya sheka daga wannan jam'iyya zuwa wata, abu ne mawuyaci magoya baya, su bi,'' in ji Mista Dixit.

Ya ce, ''ta hanyar tayar da wannan batu na wannan wurin ibada, Mista Shinde na fatan samun goyon bayan ainahin magoya bayan jam'iyyar Shiv Shena domin ya hada da na mabiya Hindu.''

Ra'ayin mabiya addinin Hindu da BBC ta yi magana da su ya rarrabu kan kalaman na Mista Shinde.

Misali, Kushal Misl, na ganin Mista Shinde ya tabo inda yake masa kaikayi, domin a wurinsa abu ne da ya yi amanna cewa wuri ne na wani wali na mabiya Hindu, wanda Musulmi suka kwace a lokacin da suka mamayi Indiya.

Haka shi ma Rajendra Gaikwad yana da irin wannan ra'ayi amma kuma ya ce ba ya jin dadi game da ce-ce-ku-cen da ake yi game da wurin a yanzu.

Ya ce, ''duk abin da ke faruwa yanzu a Indiya ba abu ne da ya dace ba,'' yana mai nuna muhimmancin zaman tare da mutunta addinin juna, inda ya kara da cewa, '' dukkanin abubuwan bauta abu daya ne.''

Shi kuwa Abhijit Nagare, wanda ke ziyartar wurin a kowa ne wata ya ce bai damu ba ko wane addini ne yake da wurin ba, inda ya kara da cewa shi dai yana jin dadin ziyartar wurin saboda yana samun natsuwa da kwanciyar hankali.

Daya daga cikin manyan amintattun da ke kula da wurin, Nasir Khan, ya gaya wa BBC cewa ce-ce-ku-cen da ake yi ta sa an samu raguwar masu ziyartar wurin sosai.

Ya ce mutane suna zuwa wurin da iyalansu to amma ba sa son bata-gari su ci mutuncinsu .

Haka kuma takaddamar ba ta tsaya a nan ba domin hatta harkokin kasuwanci a yankin ta shafa.

Wannan wurin ibada mai muhimmanci ba shi kadai ba ne a can kan tsaunin da ke da tsawon kafa 3,000, domin akwai gidaje da shaguna da wuraren cin abinci da aka sassaka a jikin dutsen tsawon shekaru.

Mista Khan ya ce kusan mutum 4,000 ne tsakanin Musulmi da mabiya Hindu ke zaune a can.

Rayuwar mazauna yankin ta dogara ne ga 'yan yawon bude idanu da ke ziyartar wurin, amma kuma fa suna wahala.

Mutanen sun gaya wa BBC cewa suna fama wajen samun abubuwan more rayuwa kamar ruwan sha mai kyau, musamman ma a lokacin tsananin bazara.

''Dole sai an rika ririta ruwan da ake da shi inda ake bai wa kowa ne gida lita 10 kawai a kullum, in ji Ayyub Shaikah, daya daga cikin 'yan majalisar kauyen.

Haka kuma babu wani cikakken asibiti ko makaranta ko ma motar daukar maras lafiya a tsaunin.

''Duk mai ilimi ba zai so ya rayu a nan ba; domin babu abin da zai yi,'' in ji wani mai tukin babur mai kafa uku da ake kira tuk-tuk a can, mai suna Shaik, wanda ya bukaci a fadi sunansa daya kawai.

Ya kara da cewa, '' abin da 'yan siyasa ke son yi kawai shi ne wasa da hankalin mutane domin su samu kuri'a. Ba wanda ya damu da abin da mutanen wurin ke bukata.''

Mutanen wurin da dama su ma abin da suke fada kenan

Shaik ya ce, ''mabiya addinin Hindu da Musulmi suna rayuwa a kan wannan tsauni shekara da shekaru cikin kwanciyar hankali da mutunta juna,''

''Muna bukukuwa tare muna kuma taimaka wa juna a lokacin wata bukata''

''Ba wanda ya damu da mu to saboda me za mu yi fada a tsakaninmu?'' In ji shi