Lafiya Zinariya: Shin kin san abinci mai gina jikin da ya dace da mai ciki?
Lafiya Zinariya: Shin kin san abinci mai gina jikin da ya dace da mai ciki?
An wallafa
Mace mai juna biyu bata buƙatar bin wani tsarin cin abinci na musamman, sai dai akwai buƙatar ta dinga cin abinci mai gina jiki da zai ba ta ƙoshin lafiya tare da jaririnta, a cewar masana.
Sun kuma bayyana cewa, an kasa abinci gida shida, kuma dole mai ciki ta dinga haɗa waɗannan abinci tana ci.
Mafi muhimmanci a cikinsu shi ne cin kayan marmari ko kayan itace da kuma ganyayyaki, musamman korayen ganyayyaki.
Cin abinci mai inganci da ke gina jiki zai kare mai juna biyu da jaririnta daga wasu cututtuka, ciki har da cutar tamowa, In ji likitoci.
Domin jin rabe-raben abinci da yadda masana ke bayar da shawarar haɗa su don samun abinci mai gina jiki, wata masaniya kan abinci, Hajara Idris ta yi cikakken bayani kan haka.