Lafiya Zinariya: Cututtukan da ake ɗauka ta hanyar Abinci

Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
Lafiya Zinariya: Cututtukan da ake ɗauka ta hanyar Abinci
An wallafa

Hukumar Lafiya da Duniya WHO ta ce mutane na ɗaukar cututtuka fiye da 200 ta hanyar cin abincin da ya gurɓata da wasu ƙwayoyin cuta.

A sakamakon hakan mutum ɗaya cikin kowanne 10 na kamuwa da rashin lafiya a duk shekara sakamakon cin abincin da ya gurɓace.

WHO ta ce abinci kan gurɓata ne a lokacin da ake sarrafa shi ko ake jigilarsa daga wani wuri zuwa wuri, ko ma a yayin da ake cinsa.