Yadda ake koya wa 'yan Ukraine tuƙa jiragen F-16 don kai wa Rasha hari

Ƙawancen Ƙasashen Yamma ya bayyana aniyar wani shirin horas da matuƙan jiragen yaƙin Yukren don koyar da su yadda za su sarrafa jirgin yaƙin Amurka samfurin F-16 a yaƙin da ƙasarsu ke yi da Rasha.
Sai dai har yanzu babu tabbas game da ƙasashen da za su samar da jiragen yaƙin, da adadinsu, da kuma lokacin.
Samar da jiragen na F-16 ga mayaƙan Ukraine ba lallai ya kasance wani abu na sha-yanzu magani-yanzu ba, cewar shugaban dakarun sojojin saman Norway, Manjo Janar Rolf Folland.
Ya ce lamarin zai iya ɗaukar lokaci kafin Ukraine ta iya tsara dabarun sarrafa jiragen yaƙin na Ƙasashe yamma masu amfani da makamai masu sarƙaƙiya.
A cewarsa, sun gana a wani babban taron ƙawance kan amfani da jiragen sama da aka gudanar a ƙasashen Norway da Finland da kuma Sweden.
ya ƙara da cewa taron ya ƙunshi batun samar da jiragen yaƙi 150, adadin da ya zarce yawan jiragen rundunar sojojn saman Ukraine.
Janar Folland ya ce, horon ya shafi yadda za a mamaye sararin samaniya ne, domin kauce wa abin da ya kira da tsohon salon yaƙin da ke faruwa a Ukraine.
Domin samun damar yin galaba a sararin samaniya, akwai buƙatar samun ƙwarewar zamani wanda Ukraine ba ta kai ga samu ba.
Hatta samar da ƙananan jirage samfurin F-16, babban kalubale ne.
Aikin ya ɗauki matukin jirgin saman Belgium tsawon shekara uku kafin ya iya fahimtar yadda zai sarrafa jirgin na F-16.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wannan ya kunshi yadda za a koyi amfani da na'urar da ke samar da bayanai ga jirgin saman na F-16, da gano wuraren da jirgin yaƙi da kuma makamai suke.
Ukraine, wadda a halin yanzu take da matuka jiragen sama masu yawa fiye da adadin jiragen, tana fatan kammala shirin nan da watanni masu zuwa.
Pulse ya lura da fa'idar da ke tattare da aniyar ƙasashen yamma na samar da jiragen yakin ga Ukraine.
Ya buga misali da makaman da jirgin na F-16 ke dauka wadanda ke iya lalata jiragen yakin abokan gaba, da kuma jefa bama-bamai kasa zuwa wuraren da aka tsara jefawa.
"Wannan na da muhimmanci," a cewar Pulse, "saboda zaka iya amfani da dukkan makaman yakin da Nato ta tanada ta hanyar amfani da jirgin."
Sai dai akwai alamar tambaya game da yadda za a kula da jiragen.
A sansanin sojojin saman Orland, suna amfani da biyu daga cikin tsoffin jiragen yaki na F-16 domin horar da injiniyoyin da ke kula da jiragen yaki.
Wanda zai iya daukar wa'adin shekara guda, kuma zai iya zarta hakan idan za a horar da manyan makanikan jiragen yakin.
"Ba zai yiwu kawai a mika ma jirgin saman yaki ace a tafi ba!" inji Kanal Martin Tesli, kwamandan sansanin sojoji kuma tsohon matukin jirgin F-16.
Ya ce akwai wuraren daukar kaya mai girma, da wasu bangarorin jirgi, da na wasu na'urori da makamai.
Amma shi da kansa ya lura cewa akwai bukatar a zamanantar da jiragen Ukraine sabanin irin na tsohuwar tarayyar Soviet.
"A wasu lokuta, idan ba a samar musu kananan jiragen yakin ba, ba za su samu sojojin saman da za su kare kansu ba."

Justin Bronk na cibiyar Royal United Services ya ce mai yiwuwa ne Ukraine za ta bukaci taimakon hayar 'yan kwangila daga kasashen yamma domin taimaka wa tafiyar da jiragen na F-16.
Tambaya da aka saba yi ita ce wacce kasa ce za ta iya lamuntar jefa mutanenta cikin hadari a halin yanzu?
Farfesa Bronk ya kara da cewa, mai yiwuwa ne Rasha tana wani shirin kaddamar da hari kan sansanin sojojin saman Ukraine muddin aka samar da jiragen saman yaki daga kasashen yamma.
Wannan shi ne babban hadarin da ke tattare da samar da jirgin na F-16.
Hakan na daga cikin manyan dalilan da suka sa Amurka ta jima tana jure matsin lambar Ukraine na neman ta samar mata da jirgin na F-16.
Saboda fargabar yiwuwar barkewar rikici, da kuma samar da wadatattun dabarun tafiyar da jiragen yakin.
Shi ya sa cibiyar tsaron Pentagon ta yi gargadin cewa shiri ne mai sarkakiya kuma mai matukar tsada.

Mai yiwuwa ne samar wa Ukraine mayaka daga kasashen yamma zai iya ta'azzara yakin da ake fama da shi a halin yanzu.
Lt Col Neils Van Hussen, tsohon matuƙin jirgin F-16 a sansanin sojojin saman Royal Netherlands, yace, "babu wani shirin amfani da makaman da zai iya sanya akalar babban yaki".
Ya yi amanna cewa jiragen F-16s, za su taimakawa Ukraine ne kadai wajen jure abubuwan da ke faruwa a halin yanzu".
Hakikanin al'amari game da wannan yaki shi ne ko da Rasha, duk da irin karfin sojinta, ba za ta iya kankane sararin samaniya ba.
Tsarin kula da tsaron sansanin sojojin saman kasar yana taimaka mata wajen kauce wa faruwar munanan al'amurra.
Samar wa Ukraine karin matakan tsaro ta sama zai kasance babban abin da kasashen yamma za su fi mayar da hankali.
Sake gina tsarin sojojin samanta abu ne da zai dauki dogon lokaci.











