Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Foden ya tsawaita zamansa a Man City, Man UTD na sa ido kan Vardy
Dan wasan tsakiya na Ingila Phil Foden, mai shekara 22, ya sanya hannu kan kwantaragin ci gaba da taka leda na shekaru masu tsawo a Manchester City, inda za a rinka biyan sa kudin da suka kai kimanin £225,000 a kowane mako. (Mail)
Manchester United da Chelsea na sanya ido kan dan wasan gaba na Leicester City Jamie Vardy, mai shekaru 35, wanda saura shekara daya kwantaraginsa ya kare da kungiyar tasa. (90min)
Akwai alamun cewa Tottenham za ta mayar da hankali kan sayen dan wasan gefe na kungiyar Wolves, Adama Traore, mai shekaru 26, idan suka kasa cimma matsaya da Roma kan daukar dan wasan tsakiya na Italiya Nicolo Zaniolo, mai shekaru 23. (90min)
Sampdoria ta amince da tayin kudi £16.7m da Brentford ta yi mata domin sayen dan wasan tsakiya Mikkel Damsgaard, mai shekaru 22, dan asalin kasar Denmark. (Sky Sports)
Wata kungiya da ke buga babbar gasar kwallon kafar Saudiyya ta nuna sha’awar daukar dan wasan Manchester United, Cristiano Ronaldo, mai shekaru 37. (CBS Sports)
Manchester City ta fara tattaunawa da Anderlecht game da matashin dan wasa, dan asalin kasar Sifaniya Sergio Gomez, a maimakon wanda take nema Marc Cucurella, mai shekaru 24 na kungiyar Brighton. (Times - subscription required)
Brighton na tunanin sayo dan wasan baya na RB Leipzig kuma dan asalin kasar Sifaniya Angelino a matsayin makwafin Cucurella, wanda kungiyar Chelsea ma ta nuna tana so. (Sky Sports Germany, via Mail)
A karo na biyu Leicester ta ki amincewa da tayin kudi sama da £40m, daga Newcastle kan dan wasan tsakiya na Ingila James Maddison, mai shekaru 25. (Sky Sports)
Newcastle din dai tana kuma neman wani dan wasan na Leicester, wato Harvey Barnes, mai shekaru 24, wanda dan asalin kasar Ingila ne mai buga gefe. (Guardian)
Dan wasan baya na Leicester, Wesley Fofana ya nuna alamun cewa zai iya barin kungiyar wadda ke wasa a King Power Stadium, bayan da ya cire sunan kungiyar a shafukansa na sada zumunta. Dama dai Chelsea ta nuna cewar tana bukatar dan wasan, dan asalain Faransa mai shekaru 21. (Leicester Mercury)
Fulham ta mika tayinta ga Manchester United domin sayen dan wasan baya, dan asalin kasar Ivory Coast, Eric Bailly, mai shekaru 28. (Football Insider)
Chelsea ta nuna aniyar dauko dan wasan baya na Southampton, dan asalin kasar Ingila, Kyle Walker-Peters, mai shekaru 25. (Guardian)
Everton ba ta da aniyar sake dauko dan wasan tsakiya na Ingila Ross Barkley, mai shekaru 28, ko dan wasan gaba na Belgium Michy Batshuayi, mai shekaru 28, duk kuwa da cewa ana alakanta ta da ‘yan wasan biyu na Chelsea. (iSport)
Sevilla na gab da cimma yarjejeniya da Manchester United domin daukar Alex Telles, mai shekara 29. (Fabrizio Romano)
Mai tsaron baya na Chelsea, dan asalin kasar Faransa, Malang Sarr zai fi son ya tafi Monaco a maimakon Fulham, wadda ta nuna tana son daukar dan wasan mai shekaru 23. (Standard)
Sheffield United ta sha gaban Brighton, da Southampton da kuma Leicester wurin daukan dan wasan tsakiya na Manchester City James McAtee, mai shekaru 19. (Athletic - subscription required)