Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Pogba baya son a yi masa tiyata a gwiwar kafa saboda gasar kofin duniya
Paul Pogba bai amince likitoci sun yi masa tiyata a raunin da yake da shi a gwiwar kafa ba, zai koma atisaye a Juventus a makon nan.
Dan kwallon mai shekara 29 na fargabar da zarar an yi masa aikin, zai yi jinya mai tsawo da ba zai samu damar wakiltar Faransa a kofin duniya ba a Qatar.
Tawagar Faransa ce mai rike da kofin duniya da ta dauka a Rasha a 2018, kuma Pogba yana cikin 'yan kwallon da suka raka rawar gani.
Za a buga gasar kofin duniya a Qatar tsakanin cikin watan Nuwamba zuwa Disambar 2022.
Ya koma Juventus a farkon kakar nan, bayan da kwantiraginsa ya kare daga Manchester United a karshen kakar da ta wuce.
Pogba ya ji rauni a lokacin atisaye da Juventus ke yi a Amurka don shirn tunkarar kakar tamaula ta bana.
Ya buga wa Juventus wasa daya shi ne wanda ta yi da kungiyar Mexico, Chivas Guadalajara a watan jiya, wanda ya yi korafin yana jin radadi a gwiwar kafarsa.
La Gazzetta dello Sport ta ce Pogba zai yi atisaye na musammam a dakin motsa jiki da wurin linkaya, ana sa ran zai yi jinyar mako biyar.
Juventus za ta fara wasan farko a Serie A ta bana da karbar bakuncin Sassuolo ranar Litinin 15 ga watan Agusta.