Man United ta raba maki da Real Socieded

Joshua Zirkzee

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Zirkzee ne ya fara ci wa Man United ƙwallo
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ƙwallon da Joshua Zirkzee ya ci wa Manchester United ba ta iya tseratar da ƙungiyar ba a wasan da suka tashi 1-1 da Real Socieded a gasar zakarun Turai ta Europa League.

Ɗan wasan na ƙasar Netherlands ne ya fara ci wa United ƙwallo a wasan da aka buga a Sifaniya minti 12 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Sai dai Socieded ta farke ta ƙafar Mikel Oyarzabal daga bugun finareti bayan na'urar VAR ta gano cewa Bruno Fernandes ya taɓa ƙwallo da hannu.

Man United ce ta mamaye wasan, inda mai tsaron raga Andre Onana bai buge ko ƙwallo ɗaya kafin a buga masa finaretin.

Daga baya kuma Onana ya kaɗe ƙwallaye biyu masu haɗari da suka kusa bai wa Socieded nasara a wasan na zagayen farko.

Sai a ranar Alhamis13 ga watan Maris za a buga zagaye na biyu a filin wasa na Old Trafford.

Man United da Real Socieded

Asalin hoton, PA Media