Cin zarafin da 'yan aikin gida ke fuskanta
Cin zarafin da 'yan aikin gida ke fuskanta
An wallafa
A mafi yawancin ƙasashen Afirka, batun 'yar aikin gida wani lamari ne da ya zama tamkar ruwan dare a nahiyar, domin kuwa idan ba ka taɓa ɗaukar 'yar aiki ba, to ka san wanda ya ɗauka, ko kuma ka san wadda aka taɓa ɗauka a matsayin ƴar aiki a wani gida.
Sashen binciken ƙwaƙwaf na BBC Africa Eye ya bankaɗo yadda ake cin zarafin irin waɗannan yara a ƙasar Kenya.
Wata mata da muka mayar da hankali a kanta tun a shekarar 2018, ta bayyana a wani ofishin 'yan sanda, bayan ta kuɓuto daga hannun iyayen gidanta, waɗanda suka azabtar da ita tare da garƙame ta.
Ta bayyana wa 'yan sanda cewa ''idan na yi kuskure sai a maƙureni a jikin bango''



