Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Waiwaye: Abin da ya sa Najeriya ke kashe ɗimbin kuɗi a tallafin mai
Wannan maƙala ce da ke waiwaye domin kawo muku muhimman labaran da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwan da shi
Wasu ƴan siyasa ne ke agaza wa masu zanga-zanga don kawo fitina - Shettima
A cikin makon da ya gabatan ne mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya zargi wasu 'yan siyasar ƙasar da taimaka wa masu zanga-zanga domin haddasa ruɗani a ƙasar.
Shettima ya fadi hakan ne a cikin wata tattaunawa da ya yi da BBC Hausa a ranar Alhamis, yayin da wasu 'yan ƙasar suka shirya zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a ƙasar.
Mataimakin shugaban ƙasar ya ce shugaban ƙasar na fifita arewa idan aka yi la'akari da sabuwar hukumar kula da dabbobi da shugaban ƙasar ya samar saboda ƴan arewa su amfana ne, da kuam wasu muhimman muƙaman ministoci da ya bai wa 'yan yankin.
'''Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na sane da halin da al'umma ke ciki, kuma yana tausaya masu, Insha Allah gwamnati na kawo tsare-tsaren ganin cewa la'ummarmu an ɗauki matakin ƙarfafasu,'' kamar yadda Shettiman ya bayyana.
'Yanbindiga sun sace sarki da mutane 104 a Sokoto
A makon da ya gabatan ne dai bayanai daga jihar Sokoto su bayyana cewa wasu 'yanbindiga ɗauke da makamai sun kai hari ka kai hari ƙananan Bayanai sun nuna cewa a baya-bayan nan matsalar tsaron ta yi sanadiyyar sacewa da garkuwa da mutane kimanin 150, ciki har da sarkin Sabon Birnin Gobir, Alhaji Isah Muhammad.
A tattaunawarsa da BBC, ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Sabon Birni ta arewa a majalisar wakilan Najeriya, Aminu Boza, sarkin na kan hanyarsa ne daga Sokoto zuwa Sabon Birni lokacin da ya ci karo da ɓarayin waɗanda suka sace shi."
Ya ƙara da cewa a yanzu haka ƴan bindigan na neman a ba su maƙudan kuɗaɗe kafin su sake shi.
'Maƙwabtan ƙasashe ne ke sa Najeriya kashe ɗimbin kuɗi a tallafin mai'
A farkon makon ne dai ministan kuɗi da tattalin arziki na Najeriya Mista Wale Edun, ya ce ƙasar na kashe ɗimbin kuɗin da ya kai dala miliyan 600, kwakwankwacin sama da naira biliyan 956.370 a duk wata wajen siyo mai daga waje saboda makwabtan ƙasashe na cin moriyar man na Najeriya.
Ministan ya ce ƙasashen da ke amfani da man da Najeriyar ke siyowa daga waje ba wai makwabtanta ba ne na kusa har ma zuwa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya wato Santaral Afirka.
Ya ce, ''ba Najeriya kaɗai muke sayo wa ba, muna saya wa ƙasashe ta gabas, har zuwa Afirka ta Tsakiya. Muna saya wa ƙasashe na arewa, muna saya wa ƙasashe na yamma.
Sanata Ndume ya ce ya ba wa jam'iyyar APC haƙuri
A ranar Talatar makon da ya gabatan ne Sanata Mohammed Ali Ndume ya nuna nadama tare da bayar da hakuri kan sukar da ya fito fili ya yi a kan jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya da kuma kasar Bola Ahmed Tinubu.
Sai dai a hirarsa da BBC, Sanatan ya ce sun nemi afuwar juna ne shi da jam'iyyarsa ta APC wadda ta ba da umarnin cire shi daga mukamin mai tsawatarwa a majalisar dattawa a watan jiya.
Ndume ya ce sun yi wata ganawa a ranar Talata da shugabannin jam'iyyar kuma ya nemi afuwa game da kalaman sukar da ya yi a kafafen yada labarai maimakon gabatar da koken nasa ga jam'iyyar.
Gwamanan Oyo ya musanta maganar Tinubu kan tallafin kuɗi ga jihohi
A ranar Alhamis ɗin makon ne kuma gwamanan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya musanta maganar da shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya yi cewa gwamnatin tarayyar ƙasar ta bai wa jihohi, sama da naira biliyan 570, domin tallafa wa jama'a
A jawabinsa na neman kwantar da hankalin al'ummar ƙasar da ke zanga-zangar tsadar rayuwa da rashin shugabanci na gari, a ƙarshen makon jiya ne Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa ta raba kuɗin ga gwamnonin jihohin ƙasar 36, domin sauƙaƙa wa jama'a matsin rayuwa.
To sai dai gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde a wani saƙo da wallafa a shafinsa na X, a ranar Alhamis, ya ce shi dai jiharsa ba ta san da wannan kuɗi da Tinubun ya ce gwamnatinsa ta raba wa jihohi ba.
Karanta cikakken labarin a nan