Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaɓen 2023: Duk wanda ya aikata waɗannan laifukan zai sha ɗauri ko tara
Zaɓen 2023: Duk wanda ya aikata waɗannan laifukan zai sha ɗauri ko tara
An wallafa
Hukumar zaɓen Najeriya ta yi bayani kan wasu abubuwa ya kamata mutane su sani cewa bai kamata su aikata su ba a lokacin zaɓe.
INEC, na gargaɗi kan jama'a su kiyaye da waɗannan laifuka yayin da ake shirin fara babban zaɓen ƙasar a ranar Asabar 25 ga watan nan na Fabarairu.
Duk wanda aka samu da laifin keta dokokin zai fuskanci ɗauri ko tara ko ma duka biyu.