Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dankalin al'ajabi da aka ce yana kawar da talauci
Dankalin al'ajabi da aka ce yana kawar da talauci
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Shugaban China Xi Jinping ya yi nasarar ci gaba da mulki a karo na uku a ƙarƙashin Jam'iyyar Kwaminisanci a ranar Lahadin da ta gabata.
A kamfe din da ya dinga yi don ƙara masa farin jini, kafar yaɗa labaran ƙasar ta ce ya gabatar da wasu ayyukan ban al'ajabi a matalautan garuruwa na ƙasar.
BBC ta kai ziyara yankin Hebei, inda aka ce sun fita daga talauci bayan da shugaban ƙasar ya kai ziyara ya bai wa manoma shawarar sauya irin dankalin da suke amfani da shi zuwa wani nau'i mai yanke talauci.