Timo Werner zai sake komawa RB Leipzig

An wallafa

Chelsea na tattaunawa da RB Leipzig kan bayar da aron Timo Werner, domin ya sake komawa buga Bundesliga.

Dan kwallon tawagar Jamus, mai shekara 26 ya bar Leipzig zuwa Chelsea a 2020, amma ya kasa taka rawar gani a Stamford Bridge da cin kwallo 10 a wasa 56 a Premier League.

Chelsea ta kara karfin gurbin masu ci mata kwallaye, inda ta dauki Raheem Sterling daga Manchester City, bayan da ta bayar da aron Romelu Lukaku.

Sai dai kuma albashin da Chelsea ke biyan Werner, shi ne zai kawo koma baya wajen sayar dan kwallon.

Idan kuwa ya koma wasannin aro, watakila Chelsea ta rage alabashinsa, ko Leipzig ta biya wasu kudin.

A lokacin wasannin sada zumunta da Chelsea ta yi a Amurka, Warner ya sanar cewar a shirye yake ya gwada kwazonsa a wata kungiyar.

Newcastle United na son zawarcin dan kwallon Jamus, sai dai kuma albashin dan wasan ya yi mata tsada.

Eddie Howe na son daukar mai cin kwallaye biyu ko fiye da haka, wanda ya taya dan wasan Leicester James Maddison, kan fam miliyan 40.