Ku San Malamanku tare da Malam Sa'idu Hussaini Abdullahi
Ku San Malamanku tare da Malam Sa'idu Hussaini Abdullahi
An wallafa
Shirin Ku San Malamanku na wannan mako ya tattauna da Malam Sa'idu Hussaini Abdullahi Kano.
Ya ce ya yi karatu a wajen su Malam Muhammad Aminudden da sauransu.
Sun yi karatu ba irin na neman shaida ba, wanda manufar ita ce kawai neman shaidar da za ka nuna ka yi aiki ka samu kuɗi.
Ya kuma ja kunnen matasa kan ya kamata a riƙa aiki da ilimi idan an same shi, saboda aiki da ilimi shi ne mafi mahimmanci ba tarin yawanshi ba.



