Ku San Malamanku tare da Malam Muhammad Mahdi Sheik Haruna Rashid
An haifi Mallam Muhammad Mahdi Sheik Haruna Rashid a unguwar Fagge da ke jihar Kano a Najeriya.
A tattaunawarsa da BBC ya ce ya fara karatu ne a gida wajen mahaifinsa amma kuma daga baya ya tafi Daura a jihar Katsina, wajen kakarsa.
Sai kuma daga baya a shekarar 1986 inda Mallam ya ce Sayyada Maryam, wato 'yar Shehu Ibrahim Nyass ta zo Najeriya, ta tafi da su Senegal.
Neman Ilimi
Tun da farko dai Malam ya bayyana cewa ya fara karatu ne a wajen mahaifinsa, to amma tafiyar da Sayyada Maryam ta yi da su Senegal a can ya ci gaba da karatun Al-Qur'ani a wajenta har ya sauke ya kuma yi hadda a 1991.
Bayan ya yi hadda Malam Mahdi ya ci gaba da karatun sauran littattafai a wajen Sayyada Maryam da wasu malaman har 1996.
A wannan shekara ta 1996 ya samu gurbin karuta a Jami'ar Al-Azhar da ke Masar, inda ya je can har zuwa 2003 lokacin da ya kammala digirinsa na farko.
Daga nan sai ya sake komawa Senegal wajen Sayyada Maryam, har 2007, ya je ya yi aikin yi wa kasa hidima wato NYSC.
A shekara ta 2015 ya tafi Malaysia inda ya je ya yi karatun digirinsa na biyu, wanda ya kammala ya koma Najeriya a 2018.
A yanzu haka kuma yana karatun digirinsa na uku a Jami'ar Al-Nahda da ke Maradi a Jamhuriyar Nijar.
Malaman da suka koyar da shi
Bayan mahaifinsa, daga cikin wadanda suka koyar da shi akwai ita Sayyada Maryam, wadda idan ba a manta ba ita ce 'yar Shehu Ibrahim Nyass.
Akwai kuma malamai da suka karantar da shi, wadanda su ma Sayyada Maryam ce ta kai su can suke koyar da dalibai.
Daga cikin wadannan malamai ya ce akwai Malam Ghali wanda a wajensa ya fara karatun nahawu.
Ya ce sun yi karatun litattafai irin su Ahlari da Risala da Kawa'idi da sauransu, musamman a wajen shi Malam Ghali.
Sun kuma yi karatu musamman na haddar Al-Qur'ani a hannun Malam Tijjani Sa'idu, wanda dan uwan Malam Ghali ne, duka a Senegal.
Sai dai a cikin dukkanin malaman da Sayyada Maryam ta ke kaiwa suke karantar da su, Malam ya ce, wanda suka fi tasirantuwa da shi har a yanzu shi ne Ustaz Barhama Job.
Fara Aiki
Malam Mahdi ya gaya wa BBC cewa bayan ya kammala aikin yi wa kasa hidima ne sai ya samu aikin koyarwa a kwalejin gwamnatin tarayya ta Najeriya da ke garin Kazaure a Jihar Jigawa, wato Hussaini Adamu Federal Polytechnic, a 2008.
Haka kuma Malam yana koyarwa a Jami'ar Al-Nahda ta Maradi a Jamhuriyar Nijar, inda a can baya muka sheda muku cewa, yana kuma karatun digirinsa na uku wato PhD a makarantar.
Wurin da ya fi ba shi wuya a A-Qur'ani
Mallam ya ce wurin da ya wahalar da shi a Al-Qur'ani, wanda ba zai manta da shi ba, shi ne wani sumuni a Sura Al-A'raf ;
Ya ce ko a lokacin da suka gama hadda aka ji su, ''Sayyada ba ta nan ta yi tafiya da ta dawo ana gabatar da mu sumunin ta fara tambaya na.''
Haka lokacin da ya shiga wata musabaka a Masar, ma Malam ya ce, wani abin ban mamaki wannan sumini dai aka fara tambayarsa.
Surorin da ya fi so a Al-Qur'ani
Malam ya ce surorin da ya fi so suna da yawa, amma Surah Yasin da Surah An-Najm suna daga cikin wadanda ya fi so. Ya ce yana son wadannan surorin kwarai da gaske.
Abin da ya fi faranta masa rai
A yayin karatunsa ya shiga gasar haddar karatun Al-Qur'ani, inda lokacin da ya fara halartar gasarsa ta farko a Masar, ya zo na biyu a wannan gasa ta kasashen Afirka.
Wannan nasara da ya samu ta faranta masa rai sosai har yanzu yana alfahari da wannan abu, bai manta da shi ba.
Malam dai ya ce ya halarci gasar Qur'ani kusan sau biyar, inda ya zo na biyu a zuwansa na farko ta biyu ya zo na uku ta uku kuma ya zo na daya.
Haka kuma ya halarci gasar duniya a Dubai a shekara ta 2004 inda ya wakilci kasar Senegal, inda ya zo na uku a wannan gasa.
Abin da ba zai taba mantawa da shi ba
Mallam ya ce akwai lokacin da suke karatu wajen su 300 a zauren karatu, inda malamin da yake koyar da su tarihin annabawa ya yi wata tamabaya.
A lokacin yana koyar da su tarihin Annabi Dauda (AS) ya yi tambaya ko akwai wanda ya haddace aya ko sumunin da yake bayar da tarihin Annabi Dauda.
''To gabakidaya hol (hall) din aka yi shiru ba wanda ya daga hannu kusan mutum 300.
Akwai wani abokina wani Bamisire yana kusa da ni ya san cewar na yi haddar Al-Qur'ani yana ta cewa na daga hannu na ki dagawa, shi ya rike hannuna ya daga, malamin ya hango ni ya ce ka haddace na ce e, ya ce na tashi na tsaya ya ce to na karanta....'' in ji shi.
Ya ce, ''Cikin ikon Allah, Allah Ya taimake ni na karanta ban yi bata ba duk da cewa cike ake muna dalibai,''
''Bayan na gama ya rika yabon 'yan Afirka ya rika yabon Najeriya.''
Abubuwan bakin ciki
Abubuwan bakin ciki wadanda Mallam ya ce ba zai manta da su ba su ne, rasuwar mahaifinsu Shehi, da kuma rasuwar Sayyada Maryam.
Abincin da ya fi so
Abincin da mallam ya fi so, wani abinci ne na 'yan Senegal mai farin jini a kasar, wanda ake kira Thieboudienne ko ceebu jen ko kuma thiebou dieune.
Kusan shinkafa ce dafa-duka da kifi da Bahaushen Najeriya ya sani ko kuma jollof rice da Ingilishi.
Iyali
Mallam yana da mata daya da 'ya'ya shida.











