Za mu huce fushin mu a kan PSG - Arteta

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce za su soke fushin rashin nasarar da suka yi a hannun Borunemouth a gasar Premier ranar Asabar, a kan Paris St Germain - a zagaye na biyu na wasan daf da karshe na gasar Zakarun Turai.

Ya ce rashin nasarar zai iya ƙarfafa musu gwiwar a fafatawar mai zafi da ke tafe ranar Laraba.

Arteta na magana ne cikin fushi, bayan rashin nasarar duk da cewa su suka fara zura kwallo a ragar ƙungiyar a wasan da aka fafata a filin Emirates.

"Ba mu so yin rashin nasara ba," in ji shi. "Rashin nasara ta janyo mana fushi da kuma ɓacin-rai.

"Yanzu ya rage mu soke fushin ranar Laraba. Wannan shi ne abin da ya kamata mu yi."

Ƙungiyar ta yi rashin nasarar ce duk da saka dukkan zaƙaƙuran ƴan wasanta a fafatawar.

Tana da jan aiki a gabanta muddin tana son kai wa wasan karshe na Champions League.

Tana buƙatar doke PSG a gidanta a Parc des Princes, bayan rashin nasara da ci 1-0 a wasan farko a Emirates.