Nathan Tella da Osimhen ba za su buga wasan Najeriya da Afirka ta Kudu ba

An wallafa

Ɗan wasan gaban tawagar Najeriya Nathan Tella ba zai buga wa tawagar wasannin neman shiga gasar Kofin Duniya ba da za su buga a wata mai zuwa.

Tella mai taka wa Bayer Leverkusen ta Jamus wasa ya fice daga tawagar ta Super Eagleas ne bisa "dalilan da suka shafi iyalinsa", kamar yadda Super Eagles ta bayyana ranar Alhamis.

Yana cikin ƙunshin 'yan wasa 23 na tawagar da za ta buga wasa da Afirka ta Kudu da kuma Benin a watan Yuni, kuma karo na biyu kenan da zai saka rigar Najeriya bayan ya yi hakan a shekarar da ta gabata.

Tun da farko, tauraron ɗan wasa Victor Osimhen ne ya fita daga tawagar saboda raunin da ya ji, inda zai yi jinyar mako huɗu.

Hakan ta sa mai horarwa Finidi George ya kira ƙarin 'yan wasa biyu; Ibrahim Olawoyin mai buga tsakiya a ƙungiyar Caykur Rizespor ta Turkiyya, da kuma Kenneth Igboke mai buga baya ta gefen hagu a Enugu Rangers.

Yayin da Victor Osimhen da Moses Simon suka fice daga tawagar, shi ma Samuel Chukwueze babu tabbas ko zai isa sansanin Super Eagles.

Olawoyin na cikin 'yan Najeriya da suka fi taka rawa a gasar Super Liga ta Turkiyya a kakar da aka kammala, inda ya ci ƙwallo takwas da kuma taimakawa a ci uku cikin wasa 36 da ya buga.

Ɗan wasan mai hazaƙa zai iya buga wasa daga tsakiyar fili ko kuma mai kai hari, har ma da bin gefen hagu ko dama.