Hikayata: Labarin Mugun Nama 9/3/25
A filinmu na Hikayata a yau mun kawo maku 'Labarin Mugun Nama', wanda Fatima Isa da ke zaune a birnin Katsina ta rubuta, wanda kuma abokiyar aiki, Badriyya Tijjani Ƙalarawi ta karanta.
Marubuciyar ta gina labarin kan yadda wasu mazan aure ke neman matan banza a waje, duk kuwa da irin kulawar da matansu ke nuna musu a cikin gida.
Fatima Isa ta yi ƙoƙarin nuna yadda wannan matsala ta shiga tsakanin wasu ma'aurata har ta kai su ga samun saɓani, daga ƙarshe iyayen matar suka ba ta haƙuri ta ci gaba da zama a gidansa.
Matar ta yi ƙoƙarin nuna masa abin da yake yi bai dace ba, har ta ba shi damar ƙara aure, amma ya bijire, ƙarshe ya gamu da kaidin matan banza, inda wata cikin matan da yake bi ta yanke masa gaba, saboda ta gano yana neman wata matar bayan ita.
Wannan dai shi ne labari na ƙarshe a jerin labarai 15 da suka cancanci yabo, da muka saba kawo maku a duk shekara bayan kammala gasar Hikayata.