Burin Arsenal shi ne ta lashe dukkan wasan gabanta - Arteta

Asalin hoton, Getty Images
Mikel Arteta ya ce sun mayar da hankali kan lashe dukkan sauran wasan da ke gabansu a bana, duk da cewar an yi musu tazara a tseren lashe Premier League.
Gunners tana mataki na biyu a teburi da tazarar maki 15 tsakani da Liverpool, bayan da Arsenal ta tashi 1-1 a gidan Manchester United wasa na uku ba ta yi nasara ba a Premier.
Arsenal wadda kafarta ɗaya ta kai kwata fainal a Champions League, bayan doke PSV Eindhoven 7-1 a makon jiya, za ta karɓi bakuncin wasa na biyu ranar Laraba a Emirates.
Rabon Arsenal ta ɗauki Premier tun 2004, kenan damar lashe kofi a bana shi ne Champions League da ba ta taɓa lashewa ba, tuni aka yi waje da ita a FA da Carabao Cup a kakar nan.
''Za mu ci gaba da fuskantar kowane wasan da ke gabanmu da ƙwarin gwiwa,'' kamar yadda Arteta ya sanar.
Duk da ƴan ƙwallon Arsenal da ke jinya da ya haɗa da Bukayo Saka da Kai Havert, ƴan wasa shida da ban ne kowanne ya zura ƙwallo a ragar PSV.
Da zarar Arsenal ta kai zagayen gaba a gasar zakarun Turai ranar Laraba, za ta kara da ko dai Real Madrid ko Atletico Madrid a ƙwata fainal.
William Saliba yana daga cikin kashin bayan Arsenal, wanda ke taka rawar gani a kakar nan har da Premier League.
Ɗan kasar Faransa zai so Arsenal ta ɗauki babban kofi a bana a karon farko tun bayan da ta lashe FA Cup a 2020, bayan doke Chelsea.










