Ku San Malamanku tare da Malam Bishara Alhaji Dalil

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Ku San Malamanku tare da Malam Bishara Alhaji Dalil
An wallafa

An haifi malamin addinina a ƙauyen Sandiya da ke kusa da Damboa a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Malamin ya ce ya fara karatu a garin Gomari da ke Maiduguri, kafin ya fara karatun littafan Fiqihu, a wajen Malam Goni Tadai.

Mallam Bishara ya ce fannin limin da ya fi ƙwarewa a kai shi ne ilimin Nahwu, inda ya ba ya da shakkun li'irabin jimla kowace iriya ce.

Haka kuma ya ce suratul Iklass ce surar da ya fi jin dadin karantawa, saboda yadda take ɗauke da siffofin ubangiji.

A fannin hadidi kuwa, Malamin ya ce hadisin da Annabi S.A.W ke bayani kan rahamar ubangiji, wanda yake cewa Allah ya halicci rahamomi guda 100, inda ya tanadi 99 a lahira, guda ne kawai ya kawo duniya...

Mallam Bishara ya ce babban abin da ke faranta masa rai a duniya, shi ne sallah.

''Ai ina kabbarar fara sallah, farin ciki ya lulluɓeni kenan'', in ji shi.

Malamin ya ce yana da mace guda da ƴaƴa 10, sai dai guda ya rasu, yanzu akwai maza takwas mace guda.

haka kuma Malamnin ya ce babu inda yake fatan zuwa a rayuwarsa ialla Saudiyya, ya ziyarci ɗakin ka'aba, domin ibada.

Ɗaukar bidiyo ta tacewa

Fatawul Muhammad