Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mutumin da ke sana'ar haɗa aure a Kano
Mutumin da ke sana'ar haɗa aure a Kano
An wallafa
Malam Rabi'u Ado wanda aka fi sani da mai dalilin aure a birnin Kano, ya kwashe shekaru da dama yana ƙulla aure tsakanin maza da mata walau 'yan mata ko zawarawa.
Kawo yanzu Malam Rabi'u ya ce ya hada aure fiye da 500 a tsawon shekarun da ya kwashe yana wannan aiki.
Ya ce rashin son saki ko kuma rabuwar aure da yake yi ne ya sa ya fara tunanin haɗa aure.