Hamas za ta saki Ba'Amurke asalin Isra'ila a kokarin kawo karshen yaƙin Gaza

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Kasasahen Qatar da Masar sun yi maraba da sanarwar Hamas da ke cewa za ta saki ba'Amurka na karshe da ke raye cikin sauran mutanen da take garkuwa da su a Gaza, Edan Alexander mai shekara 21.

Matashin Ba'amurke wanda asalinsa dan Isra'ila ne ya shafe kwanaki kusan 600 a hannun mayakan kungiyar.

Sanarwar na zuwa ne kwana guda shugaba Trump ya soma rangadi a gabas ta tsakiya.

Qatar da Masar, da Amurka na ta kokarin shiga tsakani a tattaunawar Hamas da Isra'ila.

A wata sanarwar hadin-gwiwa, ƙasashen biyu sun ce matashin da za a saka alama ce mai karfafa gwiwa a kokarin komawa teburin tattaunawa.

Isra'ila dai taki amincewa da sharuda ko bukatun Hamas na tsagaita wuta a musayar sauran 'yan kasarta 59, wanda galibinsu gawwawaki ne.

Kafin wannan lokaci wani babban jigo a Hamas ya shaidawa BBC cewa ƙungiyar ta Falasdinawa na tattaunawa kai-tsaye da jami'in gwamnatin Amurka a Qatar.

Ofishin Firaministan Isra'ila ya ce Amurka ce ta sanar da shi batun sakin Alexander.

Haka Wani babban jami'in Falasdinawa da ke cikin tattaunawar ya ce Hamas na kyakyawar niyya za ta saki Alexander gabannin zuwan Trump yankin Gabas ta Tsakiya.

Sannan da safiyar yau Litinni za a sake tattaunawa domin cimma matsayar karshe kan sakin Alexander, wanda za a bukaci dakatar da ayyukan sojin Isra'ila na dan wani lokaci domin mika shi.

Shugaba Trump da ke tabbatar da sakin matashin a shafinsa na sada zumunta, ya ce wannan labari mai dadi ne da karfafa gwiwar tabbatuwar zaman lafiya nan gaba.

Alexander mai shekara 21 an haife shi a birnin Tel Aviv sannan ya girma a Amurka, kuma an yi garkuwa da shi ne a kan iyakar da ta hada Isra'ila da Gaza a lokacin harin 7 ga watan Oktoba.

Cikin mutane 251 da Hamas ta yi garkuwa da su, 59 har yanzu na hannuta, sannan 24 ne kawai ake kyatata zaton na raye.

Biyar daga cikinsu kuma na da takardun 'yan kasa a Amurka, wanda Alexander shi ne kadai wanda ya rage a raye a cikinsu.

A gobe Talata Donald Trump zai isa gabas ta tsakiya, kuma Isra'ila ta lashi takobin fadada ayyukanta na soji kan Hamas muddin aka gaggara cimma matsaya da zarran Trump ya kammala rangadinsa.

Kwanaki 70 kenan da Isra'ila ta datse shigar da kayan abinci da magunguna da saun kayan agaji Gaza, yanayin da kungiyoyin agaji ke cewa ya ta'azzara yunwa da matsalolin jin-kai da ka iya haifar da laifukan yaki.

Akwai dai fatan ziyarar Trump a gabas ta tsakiya ta sauya yanayin da ake ciki tsakanin Isra'ila da Hamas a Gaza.