Bahaushiya mai aiki da NSCDC da ke burge matan arewa
Bahaushiya mai aiki da NSCDC da ke burge matan arewa
An wallafa
Aisha Muhammad Yakasai na daya daga cikin matan arewacin Najeriya da suka bijire wa al’ada suka shiga aikin ɗamara inda yanzu haka kasancewarta a aikin yake burge ƴanmata kuma suke ta tururuwar shiga aikin.
Aisha mai matsayin Cif Sufiretenda a aikin ta kwashe shekaru fiye da 14 a wannan aiki.
Aisha ta ce babban abin da ya fi burge ta shi ne yadda a matsayinta na ‘yar jihar Kano take sanya kayan sarki kuma har ma hakan ya rinka janyo sauran jama’a.
“Ina wayar da kan mata su fahimci cewa aikin tsaro ba na maza ba ne kawai,” in ji Aisha.



