Juventus za ta koma buga Europa League a bana

Asalin hoton, Getty Images
Benfica za ta karbi bakuncin Juventus a wasa na biyar a cikin rukuni a Champions League da za su fafata ranar Talata.
Ranar 14 ga watan Satumba Benfica ta ci Juventus 2-1 a Italiya.
Idan anjima Paris St Germain za ta kara da Maccabi Haifa a Faransa a daya wasan rukuni na takwas.
PSG da Benfica kowacce tana da maki takwas-takwas, yayin da Juventus da Maccabi kowacce ta hada uku-uku, bayan wasa hur-hudu.
Paris St Germain za ta kai zagayen kungiyoyi 16 da zarar ta ci Maccabi ko kuma canjaras, sannan a ci Juventus.
Itama Benfica za ta kai matakin gaba idan ta doke Juventus ko suka tashi canjaras, sannan a ci Maccabi.
Da kyar idan Juventus za ta kai zagaye na biyu, illa dai ta yi ta uku a rukuni na takwas ta samu gurbin komawa buga Europa, ko idan kuma ba ta ci wasanta ba
Itama Maccabi da kyar ta kai zagayen kungiyoyi 16, amma za ta yin ta uku a rukunin, idan ba ta ci karawar ta ba.
Ranar 2 ga watan Nuwamba za a buga wasa na karshe a rukuni na takwas, inda Juventus za ta karbi bakuncin PSG, sannan a kece raini tsakani Maccabi da Benfica.










