Ɗan gidan shugaban ƙasa ya je majalisa don fuskantar bincike a Amurka

Ɗan gidan shugaban ƙasa ya je majalisa don fuskantar bincike a Amurka
An wallafa

Hunter Biden ya bai wa 'yan jam'iyyar Rifablikan mamaki, ranar Laraba lokacin da ba zato ba tsammani, ya isa gaban kwamitin sauraron bahasi a kan tuhume-tuhumen da ake yi masa na raina Majalisar Wakilan Amurka.

Kwamitin Bibiyar Ayyuka yana ganawa ne don nazari a kan wani ƙuduri da zai iya kama ɗan gidan shugaban ƙasa da raina majalisar dokokin ƙasar, saboda ya yi biris da gayyatar zuwa ya ba da bahasi.

Kyamarori sun dallare fuskar Hunter lokacin da yake tattaki zuwa cikin zauren sauraren bahasin tare da lauyansa, Abbe Lowell.

Ga alama 'yan Rifablikan sun fusata da hakan, har ma 'yar majalisa Nancy Mace ta zarge shi da samun "alfarmar da ake bai wa fararen fata".

"Ina jin kamata ya yi kawai a kama Hunter Biden a nan, sannan a ingiza shi gidan yari kai tsaye," a cewar 'yar majalisar wakilan daga jihar South Carolina. "An kafa ƙasarmu ne a kan tsarin mulkin doka da kuma ginshiƙi cewa doka za ta hau kan kowa daidai wa daida, ba tare da la'akari da ko ɗan gidan wane ne ba."

'Yan jam'iyyar Dimokrat da ke cikin kwamitin sun roƙi takwarorinsu na Rifablikan su bari ɗan gidan shugaban ƙasar, wanda ya zauna a cikin 'yan kallo, ya zo ya gabatar da jawabi. Sai dai shugaban kwamitin James Comer, wanda ya yi ta fama don ganin ya shawo kan mahalarta zaman, ya ƙi: "Ba Mista Biden ne yake doka ba, mu ne muke kafa dokoki."

Jim kaɗan kuma, sai Hunter Biden ya fice daga ginin Majalisar ba tare da ya yi jawabi a zaman sauraron bahasin ba. Ya fice daga zauren ne lokacin da 'yar majalisa mai ra'ayin riƙau Marjorie Taylor Greene ta fara jawabi.

Wakiliyar ta jihar Georgia, wadda a lokacin zaman ta nuna hotunan da Hunter Biden ya ɗauka tsirara a baya, ta kira ɗan shugaban ƙasar da "ragon maza".

Kwamitin Bibiyar Ayyukan na shirin yin nazari kan wani ƙuduri na raina majalisa nan gaba a ranar Laraba. Zartar da ƙudurin wani matakin farko ne da ke nuna cewa ɗaukacin Majalisar za ta yi muhawara a kansa.

Kafin a samu Hunter Biden da laifin raina majalisa, ana buƙatar samun ɗan ƙanƙanin rinjaye a ƙuri’ar da majalisar za ta kaɗa, wadda ‘yan jam’iyyar Rifablikan ke da rinjayen kujera biyu.

Mista Lowell, lauyan ɗan gidan shugaban ƙasar mai shekara 53, wanda ya yi masa rakiya zuwa majalisar ta soki lamirin ‘yan Rifablikan saboda amfani da Hunter Biden a matsayin “karkatacciyar kuka wajen sukar mahaifinsa”, Shugaba Joe Biden. Majalisar Wakilan mai rinjayen ‘yan jam’iyyar Rifablikan ta yi zargin cewa Hunter Biden da danginsa cikin rashin adalci suna amfana daga daɗaɗɗen matsayin siyasar babansa a Washington.

Fadar White House da kuma Hunter Biden sun musanta zarge-zargen.

An aika wa Hunter Biden sammaci don ya je ya gabatar da shaida a kaɗaice game da harkokin kasuwancinsa a batun tsigewar da aka yi wa mahaifinsa bara.