Shin kun san namijin goro ba ya ƙara wa maza kuzari?
Mutane da dama kan ci namijin goro da nfin ya taimaka musu ajen ƙarin ƙuzarin domin gamsar da iyalansu a mu'amalar aure, to sai dai masana sun ce ba haka lamarin yake ba.
Dakta Auwal Musa Umar ƙwararren likitan abinci a Najeriya ya ce bisa dukkan bincike da aka yi babu wata hujja da ke nuna cewa namijin goron na taimaka wa ƙarfin namiji, ko ƙarfin sha'awarsa.
Likitan ya kuma ce bincike ta tabbatar da cewa daɗewa ana ta'ammali da namijin goro ba ta hanyar da ta dace ba, kan haifar da matsalar rage ƙarfin ƙwayoyin halitta na haihuwa ga maza, lamarin da ka iya jamyo wa namiji matsalar rashin haihuwa.
To sai dai duka da haka, masanin ya ce namijin goro idan aka yi amfani da shi ta hanyar da ta dace yana taimaka wa lafiyar jiki ta fannoni da dama, ciki har da taimaka wa wajen buɗe ƙofofin iska ga mutumin da ke fuskantar matsalar numfashi.
Ya ƙara da cewa a ƙa'ida mutumin da nauyinsa bai haura kilogiram 60 ba, ba a so ya ci namijin goron da ya haura giram 100 ba a cikin kwana biyar.
Likitan ya ce namijin goro na da wasu muhimman abubuwa guda shida da bincike ya tabbatar.
- Yana ɗauke da sinadaran da ke bunƙasa garkuwar jiki.
- Namijin goro na ɗauke da sinadaran ta ke taimaka waken ninƙa abinci
- Sannan yana taimaka wa jiki ya samu waraka daga kumburi
- Haka kuma yana ɗauke da sinadaran da ke maganin lalurar da ke alaƙa da cutar Maleriya ko ciwon Suga
- Yana ɗauke da sinadaran da ke barazana ga ƙyanƙyashe ƙwayoyin halittar haihuwa.
- Namjin goro na ɗauke da sinadaran da ke taimaka wa numfashi.



