Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Premier League: Wa zai lashe kofin tsakanin Liverpool ko City ko Arsenal?
Gasar Premier League ta 2023/24 ta fara shiga gangara, bayan da aka buga wasannin mako na 25, kungiyoyi uku ne ke takarar lashe kofin bana.
Ranar Talata Manchester City ta ci Brrentford 1-0 a kwantan wasan Premier League, hakan ya sa kungiyar da Pep Guradiola ke jan ragama ta hau kan Arsenal a saman teburi.
Yanzu saura maki daya tsakanin City da Liverpool, wadda take jan ragama, kuma saura wasa 13 a kammala kakar bana.
A karon farko tun 2015-16 lokacin da Arsenal take ta ukun teburi da tazarar maki biyu a kakar da Leicester take ta daya bayan wasa 26, maki biyu ne ke kasancewa tsakanin ƴan ukun farko.
Karo na bakwai kenan da ba a samun tazara da yawa tsakanin masu fatan lashe Premier League, kuma karo na hudu a wannan karnin.
Yadda jadawalin teburi yake a yanzu
Teburin Premier League zuwa 21 ga watan Fabrairu
Kungiya Yawan wasa maki Rarar ƙwallaye
1. Liverpool 25 57 35
2. Man City 25 56 32
3. Arsenal 25 55 36
Wadan ne wasannin ne suka rage ?
Liverpool Manchester City Arsenal
Fabrairu Luton Bournemouth Newcastle
Maris Nott. Forest Man United Sheffield
Man City Liverpool Brentford
Everton Brighton Chelsea
Brighton Arsenal Man City
Afirilu Sheffield Aston Villa Luton
Man United Crystal Palace Brighton
Crystal Palace Luton Aston Villa
Fulham Tottenham Wolves
West Ham Nott Forest Tottenham
Mayu Tottenham Wolves Bournemouth
Aston Villa Fulham Man United
Wolves West Ham Everton
Kungiyar da Guardiola ke jan ragama kamar ta fi wasa masu zafi da za ta fuskanta nan gaba, wadda bayan ta je gidan Bournemouth ranar Asabar, za kuma ta karbi bakuncin Manchester United a Etihad daga nan ta je Anfield.
Sauran maki daya tsakanin Arsenal da City to amma Gunners tana kan ganiya, wadda ta fara shekarar 2024 da kafar dama, bayan da ta ci karawa biyar a jere kuma bajintar farko a tarihi da fara shiga shekara.
Za kuma ta ziyarci Manchester City a wasan karshe a gasar mako biyu tsakani idan ta kara da Chelsea a Emirates.
Ita kuwa Liverpool wasa daya aka doke ta ranar 4 ga watan Fabrairu a hannun Tottenham a karawa 18 baya a lik. Kungiyar da Jurgen Klop ke jan ragama za ta karbi bakuncin City ranar 10 ga watan Maris, sannan ta kai ziyara Everton mako daya tsakani a wasan hamayya da ake kira Merseyside derby.
Ko yaya ake hasashen wadda za ta lashe Premier League?
Hasashen kungiyar da za ta dauki Premier League - Opta
Kungiya Makin da ake hasashe Damar lashe kofin kaso cikin 100
1. Man City 85 49
2. Liverpool 83 36
3. Arsenal 80 14
Opta ya yi hasashensa ta bibiyar wasannin da yawan cin wasa da yin canjaras da kuma rashin nasara tare da amfani da kasuwar caca da kididdigar Opta da matakin da kungiyoyin ke kai a jadawalin kwazonsu. Wannan dama ce da suke amfani da ita a dubban lokaci don samun sakamako.
Hasashen kungiyar da za ta lashe Premier League - Nielsen's Gracenote
Kungiya Makin da ake hasashe Damar lashe kofin kaso cikin 100
1. Liverpool 85 44
2. Man City 85 42
3. Arsenal 81 14
Hasashen masana na Nielsen's Gracenote ya yi la'akari da kwazon da kungiyoyin ke yi da yadda suke a kan jadawalin matakin gasar Turai da ke fayyace wadanda ke sawun gaba a taka leda a tsakani.
Hakan ne ya ce Liverpool ce za ta yi ta daya, sai City ta zama ta biyu, kuma Liverpool ce za ta samu dama fiye da sauran, sakamakon wasannin da suka rage a gabanta.
Ko ma dai mai zai faru za a iya samun sauyi a tsakanin wadan nan hasashen, watakila sai a ranar 19 ga watan Mayu a samu sauyin da zai bayar da mamaki.