Ku San Malamanku tare da marigayi Nasir Muhammad Nasir
A wannan karon cikin shirin Ku San Malamanku mun sake kawo muku tattaunawar da muka yi da marigayi limamin Masallacin Waje na Kano, Sheikh Muhammad Nasir Muhammad.
Sheikh Muhammad Nasir ya rayu ne daga 1936 zuwa 2023, inda ya rasu a ranar 7 ga watan Yuni, 2023.
A cikin wannan tattaunawa yana da saƙo na musamman ga matasa.
Tarihin rayuwarsa
Mallam ya ce an haife shi a birnin Kano, a ranar 13 ga watan Maris na shekarar 1936.
Marigayin ya tashi ne a gaban mahaifinsa da kuma kakanninsa na ɓangaren uwa, inda mahaifin nasa ya sanya shi a makarantar allo har zuwa lokacin da ya sauke Alƙur'ani.
Bayan da ya sauke, mahaifin nasa ya ƙara kai shi wata makarantar allon, a gidan su Is'haka Rabiu, wajen Mallam Dantinƙi, inda a can ne kuma ya haddace Alƙur'ani.
A lokacin da aka gina makaranta a Ƙoƙi a 1956, Mallam ya kasance cikin ɗalibanta na farko.
Bayan nan kuma ya tafi makarantar koyon harkokin shari'a ta Kano, inda daga nan, ''sai muka ɗauki jarrabawar Law School, sai aka ce mutum biyar ake so a ɗauka, ni ne na shida.''
Ya kara da cewa: ''Ina waccan makaranta ta judiciary ban fi kwana talatin ba sai Firimiya (Sardauna) Allah ya ji kan sa, ya aiko wa principal ɗin makarantarmu Law School, cewa a nemi yaron nan Muhammad Nasir Muhammad a ɗauke shi.''
''To mu kai wannan Law School muka gama, Alhamdulillahi zuwa ɗan wani lokaci kaɗan shi ma ban daɗe da yawa ba sai Mallam Abubakar Gummi ya samar min hanyar da zan tafi Madina shekara ɗaya tal sai na dawo.''
Sanadin aminintakarsa da marigayi Ado Bayero
Mallam ya ce a duk duniya ba shi da wani amini da ya fi marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero.
Wannan alaƙa kuwa ta samo asali ne a dalilin aiki da aka tura Mallam, na mai sanya ido a kan alƙalai, inda aka nemi ya yi rantsuwa kamar yadda ka'idar aikin take amma ya ce shi ba zai rantse ba.
Wannan shi ne farkon alaƙarsa da Ado Bayero, inda ya ce a wannan dalili ne yana zaune a gida kawai sai ga direban Sarkin ya zo ya ce, Sarki yana kiran sa ya zo gidansa.
''In dai amini ne ba ɗan uwa ba, in dai amini bai kai ya shi ba wallahi, na yarda da shi ya yarda da ni masoyina ne masoyinsa ne ni, babu abin da yake haɗa mu ko ya raba mu,'' in ji Mallam.
Yawan iyalin Mallam
Mallam Nasir Muhammad Nasir, wanda ya ce surar da ya fi karantawa a Alƙur'ani ita ce Suratul Yusuf, a lokacin da aka yi wannan hira da shi ya ce yana da 'ya'ya kimanin 28 da kuma jikoki wurin 100.




