Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Napoli ta ɓarar da damar hawa kan teburin Serie A
Napoli ta ɓarar da dama hawan kan teburin Serie A a karon farko tun Fabrairu, sakamakon 0-0 da ta yi da Venezia ranar Lahadi.
Ita dai Venezia tana ta biyun karshen teburin babbar gasar tamaula ta Italiya ta kakar nan da maki 20.
Kenan Napoli ta ci gaba da zama ta biyu mai maki 61 daga wasa 29 iri ɗaya da na Inter Milan ta farko da tazarar maki uku tsakani da Atalanta ta ukun teburi.
To sai dai kuma Atalanta da Inter Milan za su fafata ranar Lahadi a gasar ta Serie A.
Venezia da Napoli sun samu damar maki a karawar a filin Pier Luigi Penzo, inda Giacomo Raspadori na Napoli ya buga tamaula ta bugi turke, shi kuwa Daniel Fila na Venezia ya buga ƙwallo amma ya yi faɗi.
A wasa huɗu baya da Venezia ta buga ƙwallo ɗaya ne ya shiga ragarta da yin canjaras da Lazio da kuma Atalanta.
Rabonda Venezia ta ci wasa tun bayan doke Cagliari 2-1 a cikin Disamba ta ci gaba da zama a mataki na 19 da maki 20.