Ku San Malamanku tare da Malam Sufyan Abdullahi Malumfashi

Bayanan bidiyo, Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Ku San Malamanku tare da Malam Sufyan Abdullahi Malumfashi
An wallafa

An haifi Malam Sufyanu Abdullahi Abdul'aziz Malumfashi a karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina da ke arewacin Najeriya a ranar daya ga watan Janairu na 1968.

A tattaunawarsa da BBC, ya ce ya fara karatu ne a gida wajen mahaifinsa amma daga baya mahaifinsa ya tura shi karatu zuwa wasu makarantu na tsaganya.

 

 Neman Ilimi

Tun da farko dai Malam ya bayyana cewa ya fara karatu ne a wajen mahaifinsa amma a wurin Malam Haruna da ke Ungwar BCJ a garin Malumfashi ya fara karatun litattafai na Fikihu da bangaren Larabci, Nahawu da ilimin Hadisai da kuma fannin Tarihi.

Ya yi karatun firamare a wata makaranta da ake kira Salau.

 

Yana aji 4  Allah ya yi wa mahaifinsa rasuwa kuma a haka ya ci gaba da karatun har matakin Jami’a.

Sai dai ya ce ya fuskanci kalubale a  lokacin da yake karatu saboda wasu suna ganin cewa ya shiga makarantar Boko ne domin gudun gona.

Wannan ne ya sa ya dauki dan kwadagon da zai rika zuwa gona domin ya iya zuwa aji.

Bayan ya kammala karatun firamare ya wuce makantar Sakandire ta Dan Rimi inda kuma a cewarsa yayin da yake karatu bai saki abin da ya taso da shi a gida ba na karatun Al-Kur'ani.

A wannan lokaci ne kuma sai musabaqa ta karatun AlKur'ani ta bullo.

A cewarsa akwai wani gidan rediyo a jihar Katsina da ya shirya makarantu irin wannan gasar.

Ya kuma ce ya rika samun nasara a kowace gasar da aka shirya.

A shekarar 1992 ne ya kammala karatun sakandire.

 

Malam ya ce surorin da suka fi wahalar da shi a AlKur'ani su ne Suratul An'am  da Nahali. 

 

Abin da ya fi faranta masa

 

Abin da ya fi faranta wa Malam rai shi ne lokacin da ya ji cewa ya samu gurbin karatu a Jami’ar Musulunci da ke Madina a 1993.

A 1997 ya kammala karatun jami’a kuma a wancan lokaci ya yi abota da wasu daga cikin manyan malaman Najeriya na yanzu.

A lokacin da ya je marigayi Shiekh Ja'afar Mahmud Adam ya kammala karatu.

Ya kuma samu malamai irin su Umar Rijiyar Lemo da Mansur Sokoto da Malam Muhammad Suliaman da Tukur Almanar da Abubakar Birni Kudu.

A 1999 ya zama Limamin Masallacin Area 11 har zuwa 2007 kuma a yanzu shi ne Limamin Masallacin Jabi, duka a Abuja.

 

Iyali

Malam yana da aure da 'ya'ya.