Gwanar girki 'yar Najeriya da ke burin kafa tarihi a duniya

Bayanan bidiyo, Latsa sama don kallon wannan bidiyo
Gwanar girki 'yar Najeriya da ke burin kafa tarihi a duniya
An wallafa

Ɗumbin 'yan Najeriya ne ke can suna jiran sakamakon abin tarihin da 'yar ƙasar kuma gwanar girki, Hilda Baci ta yi, inda ta ɗora sanwa tsawon sa'a 100, babu ƙaƙƙautawa.

Suna fatan cibiyar ayyana duk wata gagarumar bajinta ko abin tarihin duniya, Guinness World Record, za ta tabbatar da bajintar 'yar Najeriyar a matsayin girki mafi tsawo babu ƙaƙƙautawa da wani mutum ya yi a tarihin duniya.

Hilda na hanƙoron doke ƙwazon gwanar girkin Indiya, Lata Tondon wadda ta shafe tsawon sa'a 87 da minti 47 tana girki a shekara ta 2019.

Rahotanni sun ambato cibiyar na cewa tana nazarin shaidu kan ƙoƙarin da 'yar Najeriya ta yi, kuma da zarar ta kammala tantance bayanai za ta fitar da matsaya.

A yayin girkin, Hilda ta ɗora sanwa tun daga ranar Alhamis har zuwa Litinin tana girka abinci iri daban-daban har sama da 100.