Zan mayar da hankali kan bunkasa ilimi a Bauchi - Air Marshal Sadiq

Zan mayar da hankali kan bunkasa ilimi a Bauchi - Air Marshal Sadiq
An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Ɗan takarar gwamna a jihar Bauchi a inuwar jam’iyyar APC Air Marshal Sadik Abubakar mai ritaya ya ce idan ya samu nasara, babban abin da zai mayar da hankali a kai shi ne inganta ilimi domin shi ne ginshiƙin kafuwar al’umma. Tsohon babban hafsan sojin sama na Najeriyar ya ce abun takaici ne ganin yadda ilimi ya gamu da koma baya a jihar.

Sannan ya ce zai yi amfani da ƙwarewar da ya samu lokacin da yake jagorantar rundunar sojin sama ta ƙasar wajen ceto ilimi a jihar. A hirarsa da Halima Umar Saleh ɗan takarar gwamnan ya fara bayani ne kan muhimmancin na ilimi ga al‘umma.