'Mata sun fi hadarin fadawa shaye-shaye'
'Mata sun fi hadarin fadawa shaye-shaye'
An wallafa
Mata sun fi maza hadarin fadawa cikin shaye-shayen miyagun kwayoyi saboda raunin da suke da shi wajen halittarsu, a cewar likitoci.
Sauyi a kwayoyin halitta da mata kan samu lokacin al’ada da lokacin goyon ciki da cututtukan kwakwalwa da cututtuka kamar na sikila, na daga cikin dalilan da ke jefa wasu mata ta’ammali da miyagun kwayoyi.
Ko da yake maza sun fi matan shaye-shaye a Najeriya.
Haka kuma daga shekaru 14 zuwa 30, sune a yawancin lokuta, suka fi hadarin fadawa cikin wannan yanayi.
Yadda ake gane amsu shaye-shaye
- Sukan kebe kansu
- Maye na sauya yanayin maganarsu
- Idanunsu na kalawa su yi ja
- Masu shan wiwi tana sa su cin abinci ko rashin cin abinci
- Jinn jiri da kasa iya tashi
- Sauya dabi’u daga na kwarai zuwa marasa kyau.