Ana ce-ce-ku-ce kan wani gidan adana kayan tarihin Musulmai a Indiya

Mohiton Bibi ta kwashe kwanaki tana jiran dawowar ɗanta daga gidan yari.
An kama Mohar Ali a watan jiya bayan da ya buɗe wani ƙaramin gidan adana kayan tarihi a wani ƙaramin ƙauye a gundumar Goalpara a jihar Assam da ke arewa maso gabashin ƙasar.
Ya ce ya kafa gidan tarihin ne domin adana al'adun ƙabilar 'Miya' Musulmai masu magana da harshen Bengali a jihar.
Mista Ali, wanda shugaban jam'iyyar siyasa ne, ya kashe kusan rupi 7,000 domin gina gidan tarihin, inda aka zuba wasu kayayyakin amfanin gona da tufafin gargajiya.
To amma kwanaki biyu bayan buɗe gidan, sai hukumomin jihar suka rufe shi. Sannan kuma suka garƙame gidansa, suna masu zarginsa da amfani da gidan - wanda gwamnati ta ba shi domin kasuwanci- ta hanyar da ba ta dace ba.
Haka kuma 'yan sanda sun kama Mista Ali da wasu mutum biyu waɗanda suka taimaka masa wajen kafa gidan tarihin.
'Yan sandan sun ce sun kama shi ne ba saboda gidan adana kayan tarihi da ya buɗe ba, sai dan zarginsa da alaƙa da wasu ƙungiyoyin ta'addanci biyu.
Sai dai duka mutum ukun sun musanta zargin alaƙa da ƙungiyoyin ta'addanci.
Kamen ya sosa wa al'ummar Bengali Musulmai waɗanda suka ce al'amarin ya sanya su cikin ruɗani.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
''Shin mene ne ainihin laifin nasa''? tambayar kenan da mahaifiyarsa ta yi idanunta cike da ƙwallo.
Masu suka na cewa kamen wani yunƙuri ne na mayar da al'ummar saniyar-ware a jihar Assam, mai yawan al'umma da ƙabilu daban-daban, inda kuma ƙabila da asali ke taka muhimmaiyar rawa a fagen siyasarta.
Jihar Assam - wadda jihar masu magana da harshen Bengali da Assamese 'yan addinin Hindu ce, mai ƙunshe da tarin ƙabilu da yawan Musulmai - ana kallonta a matsayin jihar da ta kwashe gomman shekaru tana yaƙi da kwararar 'yan ci-rani daga maƙwabciyar ƙasas Bangladesh.
Tun lokacin da ta hau mulki a shekarar 2016, jam'iyyar BJP na neman ƙuri'un al'umar jihar ta hanyar bayyana manufofin da za su dace da 'yan addinin Hindu, lamarin da masu suka ke cewa wariya ne ga Musulman jihar.
'Yan siyasa da dama, ciki har da babban Minista Himanta Biswa Sarma, na yin kausasan kalamai a kansu.
A farkon wanna shekarar ne gwamnatin jihar ta amince da wasu ƙungiyoyin musulmi biyar a matsayin 'yan asalin jihar, abin da ya ƙara jefa fargabar cewa za a nuna wa sauran musulman jihar da ba sa cikin kowacce ƙungiya wariya.
Dr Hafiz Ahmed wani malamin musulunci ne a jihar ya kuma ce ''Musulman Bengali sun zama abin suka a siyasance''.
"Manufar ita ce nuna wa sauran al'umma cewa 'yan ƙabilar Miya ba 'yan jihar Assam ba ne, ana so a nuna cewa su maƙiya ne''.
Babban shugaban jam'iyyar BJP Vijay Kumar Gupta, ya musanta wannan zargi yana mai cewa ''wasu'' ne ke ƙoƙarin tayar da ruɗani cikin al'umma.
Ya ƙara da cewa ''an samar da gidan adana kayan tarihin ne domin adana al'adun al'ummar, to amma babu wanda ya taɓa irin haka a nan''
A faɗin yankin Asiya ana amfani da kalmar 'Miya' a matsayin girmamawa ga musulmai maza.
To amma a jihar Assam, ana amfani da kalmar kan talakawan musulmai waɗanda suka yi ƙaura daga gabashin Bengal wanda a yanzu ke cikin ƙasar Bangladesh.
Jihar dai na da nisan kilomita 900 daga maƙwabciyar ƙasar.
Mafiya yawan irin waɗannan 'yan ci-rani na zaune a gaɓar tekun Brahmaputra, inda mutane da dama daga wasu ƙabilun ke zaune.

Da yawan mazauna yankin ƙananan manoma ne talakawa waɗandsa suka dogara a kan aikin fito daga kogi domin samun abin da za su ci.
Suna fuskantar wariya kuma ana yi musu kallon 'yan kaka-gida da ke ƙoƙarin ƙwace sana'o'i da gonaki da kuma al'adun mutanen jihar Assam da ƙabilunsu.
To amma a shekarun baya-bayan nan al'ummar musulmin Bengali sun rungumin tarihi da al'adunsu, tare da ƙoƙarin maido da martabar kalmar 'Miya' ta asali da ake yi wa mazajen cikinsu.
Gidan adana kayan tarihin da ke ƙauyen Goalpara, an kafa shi ne a wani ƙaramin ɗaki, inda aka sanya wasu 'yan kayayyakin noma, da kayan kamun kifi, da wasu tufafin al'ada, waɗanda duka mista Ali ya ce suna daga cikin kayyakin al'adun Miya.
To amma shugabannin jam'iyyar BJP sun zarge shi da ƙoƙarin haddasa rarrabuwar kawuna tsakanin al'ummar jihar suna masu cewa gidan tarihin ya ƙunshi kayayyakin al'adun jihar Assam, ba na ƙabilar al'umar musulman Miya masu magana da harshen Bengali ba.
"Shin akwai wata al'umma da ake kira Miya?" kamar yadda babban ministan jihar ya faɗa a watan da ya gabata, sa'o'i kafin rufe gidan tarihin.

End of Ƙarin labarai masu alaƙa
Sherman Ali Ahmed ya shaida wa BBC cewa a tunaninsa bai dace Mista Ali ya buɗe gidan adana kayan tarihi a gidan da gwamnati ta ba shi ba, to amma hukuncin da aka yi masa ya yi tsauri.
"Bai aikata wani babban laifi ba, amma gwamnati na ɗaukar tsattsauran mataki a kansa da ma wasu domin razanar da al'ummar''.
Dakta Ahmad ya yi zargin cewa gwamnati na ƙoƙarin amfani da yawan ƙabilunsu wajen cutar da al'ummar waɗanda suka daɗe suna fargabar cewa za a mayar da su 'yan ci-rani ta hanyar raba kan al'ummar jihar.
A yayin da mutanen ƙauyen su Mista Ali ke ci gaba da fuskantar kamen jami'an tsaro, da yawa daga cikinsu sun ƙi cewa komai game da gidan adana kayan tarihin.
Inda wasu ke cewa ba za su yadda ce-ce-ku-cen da ke tattare da gidan tarihin ya shafi rayuwarsu ba.
Wani mazaunin yankin mai suna Shaheed Ali, ya ce "Mu ba gidan tarihi muke da buƙata ba, muna buƙatar ayyukan yi da hanyoyi da wutar lantarki''.
Dakta Ahmad ya ce duk da cewa gidan adana kayan tarihin nasa bai saɓa wa ƙa'ida ba, mutanen yankin na da damar adana tarihinsu.
"Bayan shafe shekaru suna fuskantar muzgunawa, al'ummar musulman Miya na ƙoƙarin fito da tarihinsu'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa ta yaya al'umma za ta wanzu ba tare da al'adunsu ba?










